Hotunan taron Shugabannin EU-AU a Abidjan

Shugabannin Kasashen Turai da Afirka sama da 80 suka kwashe yammacin jiya suna tafka mahawara kan yadda za’a kawo karshen matsalolin da suka addabi nahiyar, musamman matsalar cinikin bayin da ta taso a Libya.

Shugabanni EU-AU da ke halatar taron Abidjan

Waziriyar Jamus Angela Merkel tsaye tare da Teodoro Obiang Nguema na Equatorial Guinea da Mahamadou Issoufou na Niger da Ibrahim Boubacar Keita na Mali

Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara tare da shugaban Majalisar Turai Antonio Tajani

Sakataren harkokin wajen Burtaniya kenan Boris Johnson lokacin da ya isa Abidjan

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a lokacin da takwaransa na Ivory Coast Alassane Ouattara ke tarbansa

Mataimakiyar Shugaba Gambia Fatoumata Tambajang da shugaba Gabon Ali Bongo Ondimba

A cikin wannan hoton akwai Jacob Zuma na Afirka ta kudu da Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai Donald Tusk daga hannun dama

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa na zantawa da sarkin Moroko Mohammed VI, A bayansu akwai Shugaban Gabon Ali Bongo Ondimba da takwaransa na Kamaru Paul Biya

Shugaban Kasar Guinea Alpha Conde tare da wasu shugabannin Afirka a Taron EU-AU a Abidjan

Waziriyar Jamus Angela Merkel da Shugaban Afirka ta kudu Jacob Zuma lokacin bude taron

Daya daga ciki masu tarban baki a taron