Hotunan murnar kawo karshen mulkin Mugabe a Zimbabwe

Al'ummar Zimbabwe na ci gaba da murnar kawo karshen mulkin Robert Mugabe wanda ya shafe shekaru 37 akan karaga. Mugabe ya yi murabus ne bayan ya sha matsin lamba daga sojoji da kuma al'ummar kasar. An zargi Mugabe da kokarin bai wa matarsa Grace Mugabe damar gadon shugabancin kasar, abin da ya sa ya kori mataimakinsa, Emmerson Mnangagwa. Koran Mnangagwa ne ya tayar da guguwar ganin cewa Mugabe ya sauka.

Jerin matasa na nuna farin ciki kan murabus din Mugabe a Harare

Wani bangare na gungun matasa da ke nuna murnarsu a Harare bayan saukar Mugabe daga karaga

Wasu daga cikin mambobin Majalisar Dokokin Zimbabwe na murna jim kadan da murabus din Mugabe

Lokacin da Majalisar Zimbabwe ke karanta takardar murabus din Mugabe

Mata na daga cikin masu murnar kawo karshe mulkin Mugabe

Lokacin da ake zanga-zangar ganin Mugabe ya sauka

Wani bangare na jama'ar Zimbabwe da ke neman Mugabe ya sauka

Masu zanga-zanga dauke da hoton Mugabe a harabar Majalisar Dokokin kasar

Sojoji sun taka rawa wajen ganin Mugabe ya sauka

Da farko Mugabe ya ki sanar da murabus dinsa a jawabin da ya yi ta kafar talabijin

Mambobin jam'iyyar ZANU-PF mai mulki na murna a lokacin da sojoji suka yi wa Mugabe daurin talala

Masu zanga-zanga na nuna goyon bayansu ga sojojin kasar

Masu zanga-zanga na nuna goyon bayansu ga sojojin kasar

Masu zanga-zanga na nuna goyon bayansu ga sojojin kasar

Jaridun Zimbabwe sun mayar da hankali kan rikici siyasar kasar

Ana zargin Mugabe da kokarin bai wa matarsa Grace Mugabe damar gadon kujerar mulkin kasar

Robert Mugabe da matarsa Grace Mugabe a wajen taron jam'iyyarsu ta ZANU-PF

Emmerson Mnangagwa da Robert Mugabe ya kora a matsayin mataimakinsa