Yadda zanga-zangar 'yan adawa ta kasance a Kenya

Mutane kusan 20 suka jikkata a zanga-zangar da ‘yan adawa suka kaddamar a kenya, bayan jagoransu Raila Odinga ya sanar da janyewa daga zaben shugaban kasa da ake shirin sakewa tsakanin shi da shugaba Uhuru Kenyatta.

'Yan sanda na amfani da hayaki mai sa kwala kan masu zanga-zanga

Masu zanga-zanga sun cafke wani Barawo a cikinsu

Magoya bayan Raila Odinga sun fantsama kan tittuna Nairobi

'Yan sanda a kokarinsu na tarwatsa masu zanga-zanga

Jami'an tsaro sun cafke daya daga cikin masu bore

An yi amfani da hayaki mai sa kwala kan wadanda suka fito domin nuna adawarsu da janyewar Raila Odinga daga takara

'Yan sanda na harba hayaki mai sa kwala

Jami'an tsaro na arangama da masu zanga-zanga