Isa ga babban shafi
Guatemala

Mutane 30 sun mutu, wasu 600 sun bata, sakamakon a zaftarewar kasa a Guatemala.

A kalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu a kasar Guatemala a yayinda wasu sama da 600 suka bata sakamakon zaftarewar kasa da ta rutsa da daruruwan gidajen zaman jama’a dake kusada babban birnin kasar

masu aikin ceto a kasar Guatemala
masu aikin ceto a kasar Guatemala
Talla

Yanzu haka dai sama da masu aikin ceto 500 ne, ke ci gaba da kokarin tono wadanda hadarin ya  rutsa da gidajensu, bayan da aka dakatar da  aikin ceton a daren jiya juma'a

Hadarin dai ya faru ne, tsakanin daren shekaranjiya Alhamis zuwa safiyar jiya juma’a, a wani wuri mai tazarar kilo mita 15 gabashin Santa Catarina Pinula babban birnin kasar ta Guatemala
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.