Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Yadda tsananin zafi ya ci karo da lokacin azumin watan Ramadana
Shirin a wannan mako zai ba da hankali ne akan tsananin zafin da ake fama da shi a wasu yankuna na Nahiyar Afirka, a wannan shekarar ya tsananta inda a wasu sassa na tarayyar Najeriya lamarin ya dan wuce misali.Jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya, jiha ce da tun asali aka sani da tsanantar kowane juyin yanayi na Zafi ko na Sanyin Hunturu ko ma na yawan saukar Ruwan sama.Sai a latsa alamar sauti domin sauraron shirin.07/04/202420:04 -
Kaddamar da shirin inganta harkokin noma a jihar Niger
Shirin na wanna makon zai yi dubi ne akan katafaren shirin zamanantar da aikin noma da gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta kaddamar. Masana na ganin Jihar a matsayin wadda idan aka tattala kasar noma da take da ita, a cikinta kadai za a iya noma abincin da zai iya ciyar da kasar har ma a iya fitarwa zuwa kasashen ketare.31/03/202420:13 -
Najeriya ta kasance kan gaba a fagen noman masara a yankin yammacin Afrika
Shirin wannan mako zai ba da hankali ne a kan yadda Najeriya ta kasance akan gaba a fagen noman masara a daukacin yankin yammacin Afrika, inda kasar ke samar da sama da kashi 48 na masarar da ake nomawa a yankin.Mafi yawan masarar da ake nomawa a kasar, na fitowa ne daga yankin arewacin kasar, musamman jihohin Bauchi, Kaduna, Borno, Naija da Taraba da kuma wasu ‘yan kalilan din jihohin kudu maso yammacin kasar.23/03/202421:02 -
Shiri na musamman kan yadda bangaren noma ya fuskanci matsaloli a Najeriya
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" a wannan mako na musamman ne, domin kuwa ya yi dubi ne a kan matsaloli da dama suka addabi bangaren noma a Najeriya, wanda ake ganin su suka hana kasar samarwa kanta abincin da zai wadata jama'arta musamman a wannan lokaci da ake fuskantar tsadar sa a kasuwanni.16/03/202419:59 -
Yadda wasu suka rungumi sana'ar kiwon Dodon kodi a yankin Naja Delta
Shirin mu na wannan mako zai yi duba ne a kan batun yadda wasu suka rungumi sana'ar kiwon Dodon kodi a yankin Naja Delta da ke tarayyar Najeriya musamman a jahar Cross River.Wakilin mu dake yankin MURTALA ADAMU ya kai ziyara a wa ta Gona da ake wannan kiwon kuma ya zanta da wadanda suke sana'ar, wa ta da ta rungumi sana'ar ta yi bayani dalla dalla yadda ake fara tsara kiwon da kuma abubuwa da suka dace a tanada.24/02/202417:26 -
Halin da yankunan da suka gamu da iftila’in ambaliya ke ciki a Najeriya
Shirin awannan mako zai maida hankali ne kan batun halin da yankunan da suka gamu da iftila’in ambaliya ke ciki a Najeriya, tare da duba matakan da suke dauka na kare kai anan gaba.Idan ba a manta ba dai Shekara guda kenan da faruwa mummunar ambiyar ruwa a wasu jihohin Najeriya, kuma jihar jigawa dake arewacin kasar na cikin jihohin da ambaliyar tayiwa barna10/02/202420:09 -
Gwamnatin Najeriya ta kudiri aniyar amfani da noman alkama don samar da aikin yi
A wannan mako shirin zai yi dubi ne akan shirin gwamnatin Najeriya na bunkasa noman alkama domin yaki da talauci da kuma wadata kasar da abinci.A wani mataki na kawar da matsalar zaman kashe wando da magance rashin aikin yi musamman tsakanin matasa, gwamnatin Nigeria ta kuduri aniyar amfani da noma wajen samar da guraben aikin yi wa dubban matasan da basa da abin yi a fadin kasar.29/01/202419:28 -
Hasarar da manoma suka samu a yayin girbin kayayyakin da suka noma a Najeriya
Hasarar da manoma suka samu a yayin girbin kayayyakin da suka noma a Najeriya wadda gwamnatin kasar tace yakan kai sama da Nera triliya 3 a kowacce shekara .Sashen Hausa na Radio France International ya yi tattaki zuwa jihar Kano a Najeriya inda muka gana da masu ruwa da tsaki domin jin yadda ta kaya a wannan karowandada suka kuma bayyana cewa anfi samun asarar mafi girma akan kayan lambu amma hakan bai tsaya a bangare guda ba domin hatsi ma ba a barshi a baya ba20/01/202420:59 -
Hukumar hasashen yanayin Najeriya ta ce za a fuskanci bahagon yanayi a kasar
Shirin wannan mako zai yi dubi ne yadda Hukumar da ke kula da harkokin hasashen yanayi ta Nigeria, ta yi hasashen samun wani gagarumin sauyin yanayi a yankunan arewa maso gabas da arewa ta tsakiya cikin ‘yan kwanaki masu zuwa. Bugu da kari hukumar, ta bayyana cewa shima yankin kudancin Nigeria zai shiga yanayi na zafin rana da wasu alamun hadari, kana yankunan da ke kusa da ruwa, za su shiga yanayi na hazo da ganin alamun hadari.15/01/202420:04 -
Yadda manoman Najeriya suka tafka hasara a daminar bana
A yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan batun hasarar da manoma suka samu a yayin girbin kayayyakin da suka noma a Najeriya wadda gwamnatin kasar tace yakan kai sama da Nera triliya 3 a kowacce shekara .31/12/202319:17 -
Koma bayan da manoman Najeriya suka samu a kakkar girbi na Shekara ta 2023
Shirin a wannan karo zaiyi dubi ne akan wasu bayanan kididdiga da suka yi nuni da cewa kakar noma ta shekara ta 2023, na daga cikin lokaci mafi muni ga mafi yawan manoman Nigeria a sakamakon matsalar sauyin yanayi da ta haifar da karancin ruwan sama.A halin yanzu dai, wata babbar kungiyar kasa da kasa mai suna Action Aid, ta bayyana cewa irin hasarar da manoman Nigeria suka dibga a bana ta haura Nera Trilion 3, a daidai lokacin da ake fama da tsadar kayan abinci a kasar.18/11/202319:59 -
Amurka da Norway za su tallafawa manoman Afirka da dala miliyan 70
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" tare Nasiru Sani, a wannan mako ya yi dubi ne a kan gidauniyar kudade daya kai dalar amurka miliyan 70 da kasar Amurka da Norway zasu samar don inganta harkan noma a nahiyar Afrika.04/11/202319:01 -
Yadda aka horas da manoma dabarun yaki da matsalar dumamar yanayi a Najeriya
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" tare Nasiru Sani, ya maida hankali ne kan yadda gwamnatin Najeriya karkashin ma'aikatar albarkatun ruwa da Bankin Raya Afrika suka horar da manoman karkara dabarun noma na zamani, wanda za su taimaka wurin yaki da dumamar yanayi da a yanzu duniya ke fama da shi wato Climate Change a turance.Wannan horo da aka baiwa wadannan matasa karkashin shirin na hadin gwiwa da ake kira da PIDACC, ba wannan shi ne karon farko da aka fara gudanarwa ba.28/10/202319:50 -
Yadda 'yan kasuwa ke sayen kayan abinci domin jiran kazamar riba
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" tare Nasiru Sani, ya maida hankali ne kan yadda 'yan kasuwa a Tarayyar Najeriya musamman arewacin kasar, ke shiga kasuwanni da makudan kudi domin saye kayayyakin abinci, su kuma boye domin jiran lokacin da kayan za su yi tsada a kasuwanni kafin su fara fitowa da su da zummar samun kazamar riba, ba tare da la'akari da matsanancin hali da talakawan kasar ke fama da shi ba.21/10/202319:25 -
Yadda sauyin yanayi ke haddasa wutar daji da kafewar koguna sakamon tsananin zafi
Shirin Muhallinka rauwarka tare da Nasiru Sani ya mayar da hankali ne kan sauyin yanayi wanda ya haddasa tsananin zafin da yanzu haka ya addabi kasashe da dama musamman a yankunan Turai nahiyar Asiya da kuma Afrika wada tuni ya haddasa gagarumar illa ta hanyar kafar da tarin koguna a mabanbantan yankuna.07/10/202319:56
Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).