Mu Zagaya Duniya
Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Hukumar EFCC na neman tsohon gwamnan jihar Kogi Yahya Bello ruwa a jallo
Daga cikin labarun da shirin karshen makon ya waiwaya akwai neman tsohon gwamnan jihar Kogi yahya Bello da hukumar EFCC ke yi ruwa a jallo, lamarin da ya kai ga daukar matakin dakile duk wani yunkurinsa na ficewa daga Najeriya20/04/202420:05 -
Muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata
Masu sauraro daga sashin Hausa na RFI cikin shirin Mu Zagaya Duniya da saba zabo wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata, domin bitarsu.A ranar Larabar da ta gabata al'ummar Musulmin Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na duniya wajen gudanar da Sallar Idi Karama, wadda aka saba gudanarwa bayan kammala azumin watan Ramadan.13/04/202420:01 -
Karin kudin wutar lantarki ya fusata 'yan Najeriya
Shirin Mu zagaya duniya na wannan mako ya duba batun karin kudin wutar lantarki a Najeriya, halin da ake ciki a Gabas ta tsakiya da kuma rikicin siyasar Togo.06/04/202419:40 -
Bitar labaran mako: Yadda aka ceto daliban Kuriga a Kadunan Najeriya
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako tare da Rukayya Abba Kabara ya yi bitan wasu daga cikin labaran da suka fi daukar hankali a makon da ya wuce ciki har da labarin yadda gwamnatin Najeriya ta ceto daliban Kuriga da ke Jihar Kaduna tare da sada su da iyalan su.30/03/202419:30 -
Dubi akan matakin gwamnatin mulkin sojin Nijar na katse huldar aiki da dakarun Amurka
Daga cikin muhimman batutuwan da shirin ya waiwaya a wannan makon akwai matakin Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar na kawo karshen yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasar da Amurka.23/03/202419:13 -
Matakin Najeriya na bude iyakokin da ta rufe tsakaninta da Jamhutiyar Nijar
Daga cikin labarun da shirin ya kunsa a wannan makon, akwai matakin da Najeriya ta dauka na bude iyakokin da ta rufe tsakaninta da Jamhutiyar Nijar, tare da janye baki dayan takunkuman da ta kakaba mata.Gwamnatin Birtaniya ta ce a shirye take ta baiwa ‘yan dubban ‘yan Rwanda da ke neman mafaka fam dubu uku kowannensu, to amma fa a bisa sharadin za su amince a mayar da su gida daga kasar ta Birtaniya16/03/202419:19 -
Wasu daga cikin muhimman labarun da suka wakana a makon da ya gabata
Za a ji yadda aka sake zabar sabuwar ranar gudanar da zaben shugabancin kasar Senegal,Al’ummar Sudan ta Kudu sun tsallake rijiya da baya, domin kuwa aniyar wani sabon mugu da ya bayyana ce ta watse bayanda ya yi kokarin shirya juyin mulki a kasar, duk da cewar har yanzu basu gama murmurewa daga kazamin yakin basasar da ya tagayyara su ba, wato dai ana kukan targade karaya kuma na neman kunno kai.09/03/202420:02 -
Wasu daga cikin muhiman labaren mako daga Rfi- Rikicin jihar Kano
Al’ummar Jihar Kano dake Najeriya sun tashi da labarin murabus din da shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi daga mukamin sa, sakamakon abinda ya kira sanyaya masa gwuiwar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi, wajen sukar yadda suke gudanar da aikin su.Wannan murabus din ta haifar da mahawara mai zafi a ciki da wajen jihar Kano, tare da hudubobi a Masallatan Juma’a dangane da muhimmancin hukumar da kuma rawar da take takawa.Nasirudeen Muhammed zai jagoranci shirin.02/03/202420:21 -
Jana'izar ma'aikacin RFI Hausa, Mahammane Salissou Hamissou a garin Tsibirin Gobir
A jiya Juma'a 17 ga watan Fabrairun 2024 ne aka gudanar da jana'izar ma'aikacin RFI Hausa, Mahammane Salissou Hamissou a garin Tsibirin Gobir, Mahammane Salissou Hamissou wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Larabar da ta gabata sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.17/02/202420:10 -
Matakin hadin gwiwar da Nijar ,Mali da Burkina Faso suka dauka, na sanar da ficewa daga ECOWAS
Daga cikin muhimman labarun makon jiya da shirin ya sake waiwaya domin bitarsu akwai, matakin hadin gwiwar da Nijar da Mali da kuma Burkina Faso suka dauka, na sanar da ficewa daga kungiyar ECOWAS.Sai kuma sake karya darajar Naira da gwamnatin Najeriya ta yi, karo na biyu cikin watanni 8.A Turai kuwa, za a ji yadda zanga-zangar manoma ta bazu zuwa sassan nahiyar saboda adawa da wasu sauye-sauyen mahukuntan kasashen yankin da suka ce ba za su lamunta ba.03/02/202419:58 -
Taron Shugabannin arewacin Najeriya don lalubo hanyar magance matsalar tsaron
Masu sauraro Assalamu alaikum, Nura Ado Suleiman daga sashin Hausa na RFI ke muku maraba cikin shirin Mu Zagaya Duniya da ke waiwaye gami da zabar wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata, domin bitarsu.27/01/202419:56 -
Rikici tsakanin 'yan ta'adda a arewacin Najeriya ya illata bangaren Dogo Gide
Shirin wannan makon zai fara ne da waiwayar bata-kashin da aka yi tsakanin ‘yan bindiga a Najeriya, lamarin da ya kai ga illata bangaren daya daga cikin jagoran ‘yan ta’adddan da ya addabi jama’a.Fira Ministan Jamhuriyar Nijar ya yi tatttaki zuwa Iran, bayan ganawarsa da mahukuntan kasar Rasha inda suka karfafa yarjejeniyar tsaron da suka kullla.20/01/202419:49 -
Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Abba Gida-Gida a zaben gwamnan Kano
Cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Nura Ado Suleiman, ya fara ne daga Kano a Najeriya, inda a ranar Juma’ar da ta gabata, kotun koli ta tabbatar da gwamna Abba Kabir Yusuf Abba na jam’iyyar NNPP a matsayin halastaccen gwamnan jihar.15/01/202420:01 -
Gwamnatin Najeriya ta haramta karbar shaidar karatun digiri daga Benin da Togo
Daga cikin labarun da shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya sake waiwaya a wannan makon akwai matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na haramta karbar takardun shaidar kammala karatun digiri daga jami'o'in Jamhuriyar Benin da kuma kasar Togo.15/01/202419:45 -
Bitar wasu muhimman labaran da suka faru a duniya cikin wannan mako
Daga cikin labarun da Shirin ya kunsa akwai batun yadda yan ta'adda a Najeriya ke gina ramu suna boyewa, saboda barin wutar da suke sha daga sojojin kasar, sai kuma batun kammala ficewar sojojin Faransa a Nijer da dai sauran manyan labaran da suka hada da Burkina Faso, jamhuriyar Benin, yakin Isra'ila da Hamas, tare da dokar yan ci rani da Faransa ta amince da ita.23/12/202320:04
Mu Zagaya Duniya
Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.