Bakonmu a Yau
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Dr Yahuza Getso kan bukatar Tinubu ta ayyana masu satar mutane a matsayin 'yan ta'adda
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ayyana masu garkuwa da mutane a matsayin 'yan ta'adda, matakin da zai bai wa jami'an tsaro damar amfanin da karfin da ya wuce kima wajen kai musu hari. Wannan ya biyo bayan kubutar da daliban makarantar Kuriga sama da 100 da akayi garkuwa da su. Domin sanin tasirin matakin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin harkar tsaro, Dr Yahuza Getso.28/03/202403:15 -
Farfesa Jibrin Ibrahim kan zaben Senegal da aka gudanar a karshen mako
Bayanai daga Senegal sun tabbatar da Bassirou Faye 'dan shekaru 44 a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a a karshen mako, wanda zai bai wa matashin damar zama shugaban kasa mafi karancin shekaru a tarihin kasar. Wannan zabe ya dauke hankalin duniya ganin irin matsalolin da aka samu kafin zaben wanda ya kaiga rasa rayuka da kuma yadda mutumin da bai yi fice a siyasar kasar ba ya samu nasara.27/03/202403:28 -
Aminu Kuriga kan kubutar da daliban da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su
A ƙarshen makon da ya gabata ne labarin ceto ‘yan makarantar garin Kuriga ta ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna ta Najeriya da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su ya karaɗe kafafen yaɗa labarai da shafukan sadarwar intanet.26/03/202403:26 -
Hon Muktar Ishaq Yakasai kan sukar da wasu ke wa gwamnatin Tinubu
Duk da matakai da mahukunta a Najeriya ke cewa sun dauka domin tunkarar manyan matsalolin da kasar ke fama da su, da suka hada da na tsaro da kuma tsadar rayuwa, toh amma mafi yawan al'ummar kasar cewa suke yi a zahirance babu wani tasiri da wadannan matakai ke yi wajen shawo kan wadannan matsaloli.25/03/202403:37 -
Mukhtar Bello kan rikicin siyasar Senegal
A wannan Juma’a ake kammala yakin neman zaben shugaban Senegal, kasar da rikicin siyasa da ya auku a cikinta a baya-bayan nan ya gaza yin mummunan tasiri a kanta duk kuwa da jan hankalin duniya da lamarin ya yi.22/03/202403:40 -
Farfesa Tukur Abdulkadir kan ziyarar da Blinken a yankin Gabas ta Tsakiya
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya sake komawa a Yankin Gabas ta Tsakiya a ci gaba da kokarin da kasashen duniya ke yi don samar da tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas. Daga farkon wannan rikici wanda ya barke a ranar 7 ga watan Oktoban bara zuwa yanzu, sau da dama Amurka na cewa tana yunkuri domin samar da tsagaita wuta a wannan yaki da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan dubu 35 da kuma raba sama da milyan biyu da gidajensu.21/03/202403:21 -
Nastura Ashir Sharif kan kalaman da ke kokarin kawo rabuwar kai a Najeriya
Gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya CNG, ta yi zargin cewa a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsalar tsadar rayuwa, wasu ‘yan siyasa musamman a cikin majalisun dokokin kasar na furta kalamai da kuma manufofi da ke neman raba kan al’ummar kasar. Kawancen CNG ya bayar da misali da abubuwan da suka faru a zauren Majalisar Dattawan kasar bayan da Sen Abdul Ningi ya yi zargin yin cushe a cikin kasafin kudin kasar na wannan shekara, lamarin da ya kai ga dakatar da shi na tsawon watanni uku.20/03/202403:28 -
Umar Kabir Dan Anini kan katsewar sadarwar da aka samu a wasu kasashen Afrika
A makon da ya gabata ne aka samu katsewar sadarwar intanet a wasu kasashen Tsakiya da Yammacin Africa, sakamakon yankewar wasu wayoyin karkashin ruwa na sadarwar kamar yadda masana suka bayyana, lamarin da ya haifar da gagarumar koma baya a fannin tattalin arziki da harkokin yau da kullum a kasashen da matsalar ta fi shafa.19/03/202403:17 -
Farfesa Dicko Abdourahmane kan kawo karshen alakar tsaro tsakanin Nijar da Amurka
Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasar da Amurka, tare da zargin cewa dakarun Amurka wadanda adadinsu ya zarta dubu daya na zaune a kasar ne ba a kan ka’ida ba. Sanarwar ta zo ne kwana guda bayan da wata babbar tawagar Amurka ta kamma ziyarar da ta kai Nijar ta tsawon kwanaki uku.18/03/202403:39 -
Alhaji Sirajo Jankado Sarkin Hausawa Turai kan batun bakin haure
Daya daga cikin matsalolin da suka addabi nahiyar Turai a wannan lokaci, shine batun bakin haure, ganin yadda matasa daga nahiyar Afirka ke tafiya mai hadari cikin kwale kwale da zummar zuwa nahiyar, abinda ke kai ga rasa rayuka da dama. Dangane da wannan matsala da kuma matakan da magabata ke dauka wajen fadakar da al'umma illar irin wannan tafiya, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sarkin Hausawa Turai Alhaji Sirajo Jankado a fadarsa da ke kasar Faransa, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.14/03/202403:35 -
Dr Aliyu Sabi kan matakin Najeriya na sanya dokar ta baci a bangaren noma
Nigeria ta kaddamar da dokar ta baci a game da harkar noma, inda ta fidda tsare-tsare da dama don shawo kan matsalar karancin abinci da kasar ke fama da ita a cikin gaggawa, wannan kuwa ta la’akari da waharhallun da jama’a ke ciki.13/03/202403:39 -
Yahuza Getso kan fargabar gwamnatin Najeriya na kai hari karin wasu makarantu
Yayin da ake ciki gaba da samun karuwar satar dalibai a Najeriya, Gwamnatin kasar ta bayyana fargabarta tare da yin gargadin cewa za’a iya kaiwa wasu makarantu a jihohin kasar 14 har da babban birnin tarayya Abuja.Shin hakan ya nuna gazawar gwamnatin kasa ta fannin tsaro kenan? Abdulkadir Haladu Kiyawa, ya tattauna da Dakta Yahuza Ahmad Getso masanin tsaro a Najeriyar.12/03/202403:25 -
Sheikh Sani Yahaya Jingir kan fa'idar azumin watan Ramadan
A yayin da alummar musulmi daga kasashe da dama na duniya suka fara Azumin watan Ramadan, daya daga cikin manyan malaman addninin musulunci a Nijeriya, Sheikh Muhamad Sani Yahaya Jingir, ya yi karin haske akan irin fa'idar dake tattare da Azumin watan Ramadan ga abun da yake cewa a zantawarsu da wakilinmu na Jos Tasiu zakari.11/03/202402:58 -
Saudatu Abubakar kan bikin ranar mata ta duniya
Ranar 8 ga watan Maris din kowacce shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don bikin ranar mata da ke da aniyar lalubo matsalolin da mata ke fuskanta da kuma duba hanyoyin warware su.08/03/202403:31 -
Tattaunawa da Kanal Makiga kan dawowar hare-haren Boko Haram a jihar Borno
A Najeriya rahotanni daga yankin arewa maso gabashin kasar sun nuna yadda mayakan Boko Haram suka koma kai hare-hare bayan lafawar da suka yi, lamarin da ke zuwa kwanaki kalilan bayan rahoton gwamnatin jihar Borno da ya bayyana kawo karshen kaso 95 na masu akidar kungiyar ta Boko Haram.07/03/2024
Bakonmu a Yau
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.