Bakonmu a Yau
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Alhaji Shehu Ashaka kan samar da 'yan sandan jihohi a Najeriya
Mahawara na ci gaba da zafi a Najeriya, dangane da yunkurin kirkiro ‘yan sandan jihohi domin taimakawa wajen inganta tsaron lafiya da dukiyoyin jama’a. Yayin da wasu jama’a ciki harda gwamnonin jihohi da tsoffin shugabannin kasa ke cewa lokaci ya yi da za a samar da ‘yan sandan, wasu kuma ciki harda Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar na cewa har yanzu lokaci bai yi ba, saboda gwamnoni na iya amfani da su wajen biyan bukatun kan su.24/04/202403:14 -
Arewacin Najeriya aka fi kashe mutane a zangon farko na wannan shekarar - Rahoto
Wani bincike da kamfanin Beacon Securities ya yi a Najeriya, ya ce a watanni 3 na farkon wannan shekarar an kashe mutane sama da 2,500, yayin da aka yi garkuwa da wasu sama da dubu 2. Rahotan ya ce kashi 80 na wannan aika aika ana samun sa ne a yankin Arewacin Najeriya. Dangane da haka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Air Commodore Tijjani Baba Gamawa mai ritaya.23/04/202403:19 -
Farfesa Mansur Isa Yelwa kan tsarin almajiranci a Najeriya
A karshen makon da ya gabata ne zabtarewar kasa ta hallaka wasu almajirai guda 8 a Jihar Kebbi, matsalar da ta dada tado da batun kula da almajiran da ke karatun Alkur'ani. Wasu na danganta matsalar da sakacin iyaye wajen rashin kula da 'ya'yan su ko kuma ciyar da su a makarantun allon.22/04/202403:33 -
Arewa maso Yammacin Najeriya ne mafi hatsari saboda matsalar tsaro - Bincike
Kungiyar 'Global Rights' ta bayyana yankin arewa maso yammacin Najeriya a matsayin mafi hadari, saboda yadda 'yan bindiga ke kisa da take hakkin Bil Adama ba tare da kaukautawa ba.18/04/202403:16 -
Kuskure ne a yi tunanin ɗagawar darajar naira ba zai ɗore ba - Dakta Kurfi
Darajar Naira na cigaba da ɗagawa a Najeriya tare da saukar farashin wasu kayayyakin abinci a wasu kasuwannin ƙasar, abinda ya sa wasu tunanin cewar tasirin saukar Dalar ne ya sanya wasu kayayyakin suka fara sauka.17/04/202403:19 -
Tattaunawa da Sanata Ikira Aliyu Bilbis kan tsaro a jihar Zamfara
Hukumomi a Najeriya daga matakin jiha zuwa na kasar baki ɗaya na daukar matakai daban daban wajen samar da zaman lafiya a jihar Zamfara, amma har ya zuwa wannan lokaci ba'a kai ga cimma biyan bukata ba.16/04/202403:26 -
Yadda rayuwa ta kasance bayan da muka faɗa hannun mayakan Boko Haram - Maryama
A ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilun nan aka cika shekaru 10 da sace dalibai mata na makarantar sakandaren Chibok sama da 250 da mayakan Boko Haram suka yi a jihar Borno.15/04/202403:17 -
Kwamred Bello Basi kan shirin gina hanyayoin zamani a Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta sanar da kashe naira biliyan 4 kan kowacce kilomita ta hanyar zamani da ake ginawa daga jihar Legas zuwa birnin Kalaba.12/04/202403:40 -
Farfesa Muntaqa Usman kan matakin korar ma'aikata da bankin CBN ya yi
Babban Bankin Najeriya CBN na ci gaba da korar wasu daga cikin ma'aikatansa, inda a cikin kwanaki 20 da suka gabata bankin ya sallami ma'aikata 117 akasarinsu manyan ma'aikata. Kan haka Bashir Ibrahim Idris ya zanta da Farfesa Muntaqa Usman, masanin tattalin arziki a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.11/04/202403:35 -
Tattaunawa da Imam Hussien bin Hycinth kan kyautata mu'amala bayan Ramadan
Yau al'ummar Musulmin Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na duniya wajen gudanar da Sallar Eid el Fitr.10/04/202403:11 -
Farfesa Mansur Isa kan darussan da ke cikin watan Azumin Ramadan
Yau Musulmin duniya ke cika kwanaki 30 da fara azumin watan Ramadana, yayin da ake shirin bukukuwan Sallar Eid el Fitr daga gobe Laraba.09/04/202403:48 -
Baba Sheikh kan matakin yi wa mayakan Boko Haram afuwa da gwamna Zulum ya yi
Gwamnatin Jihar Barno da ke Najeriya ta ce akalla mayakan Boko Haram sama da dubu 200 suka rungumi shirin ta na afuwa, inda suka aje makaman su da kuma mika kai domin horar da su da kuma sake musu tunani, kafain mayar da su cikin al'umma. Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ne ya kaddamar da shirin domin bai wa masu bukatar aje makaman su dama.08/04/202403:50 -
Abba Terab kan cire tallafin lantarki a Najeriya
Hukumar Kula da wutar lantarki a Najeriya ta sanar da cire tallafin da gwamnati ke zubawa a bangaren samar da wutar ga wasu mutane, abinda ya shafi farashin wutar.05/04/202403:40 -
Dr Abdullahi Gwandu kan fara fitar da tatatcen mai, na matar man Dangote
Matatar man hamshakin attajirin Najeriya Aliko Dangote ta fara fitar da albarkatun man fetur din da ta tace, kamar yadda daya daga cikin manyan jami’an kula da matatar da kuma kungiyar dillalan man fetur din a Najeriya suka tabbatar. A cewar jami’in, ya ce tuni suka fara rarraba wa ‘yan kasuwa man disel da kuma man jiragen sama, inda kuma ya ce litar mai miliyan 37 suke fatan cimma fara dorawa manyan jiragen ruwa, amma a halin yanzu suna iya lodin litar man miliyan 26.04/04/202403:35 -
Dr Kasim Garba Kurfi kan matakin CBN na kara yawan jarin bankunan kasar
Babban Bankin Najeriya ya bai wa bankunan kasuwancin kasar umarnin kara yawan jarin su domin tafiya da zamani, wanda ya kunshi jarin naira biliyan 50 ga bankunan shiya da kuma naira biliyan 500 ga bankunan da ke hada hada da kasashen ketare. Domin sanin tasirin wannan mataki, Abdulkadir Haladu Kiyawa ya tattauna da masanin tattalin arziki, Dr Kasum Garba Kurfi.03/04/202403:29
Bakonmu a Yau
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.