Bakonmu a Yau
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Farfesa Dicko Abdourahmane kan kawo karshen alakar tsaro tsakanin Nijar da Amurka
Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasar da Amurka, tare da zargin cewa dakarun Amurka wadanda adadinsu ya zarta dubu daya na zaune a kasar ne ba a kan ka’ida ba. Sanarwar ta zo ne kwana guda bayan da wata babbar tawagar Amurka ta kamma ziyarar da ta kai Nijar ta tsawon kwanaki uku.18/03/202403:39 -
Alhaji Sirajo Jankado Sarkin Hausawa Turai kan batun bakin haure
Daya daga cikin matsalolin da suka addabi nahiyar Turai a wannan lokaci, shine batun bakin haure, ganin yadda matasa daga nahiyar Afirka ke tafiya mai hadari cikin kwale kwale da zummar zuwa nahiyar, abinda ke kai ga rasa rayuka da dama. Dangane da wannan matsala da kuma matakan da magabata ke dauka wajen fadakar da al'umma illar irin wannan tafiya, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sarkin Hausawa Turai Alhaji Sirajo Jankado a fadarsa da ke kasar Faransa, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.14/03/202403:35 -
Dr Aliyu Sabi kan matakin Najeriya na sanya dokar ta baci a bangaren noma
Nigeria ta kaddamar da dokar ta baci a game da harkar noma, inda ta fidda tsare-tsare da dama don shawo kan matsalar karancin abinci da kasar ke fama da ita a cikin gaggawa, wannan kuwa ta la’akari da waharhallun da jama’a ke ciki.13/03/202403:39 -
Yahuza Getso kan fargabar gwamnatin Najeriya na kai hari karin wasu makarantu
Yayin da ake ciki gaba da samun karuwar satar dalibai a Najeriya, Gwamnatin kasar ta bayyana fargabarta tare da yin gargadin cewa za’a iya kaiwa wasu makarantu a jihohin kasar 14 har da babban birnin tarayya Abuja.Shin hakan ya nuna gazawar gwamnatin kasa ta fannin tsaro kenan? Abdulkadir Haladu Kiyawa, ya tattauna da Dakta Yahuza Ahmad Getso masanin tsaro a Najeriyar.12/03/202403:25 -
Sheikh Sani Yahaya Jingir kan fa'idar azumin watan Ramadan
A yayin da alummar musulmi daga kasashe da dama na duniya suka fara Azumin watan Ramadan, daya daga cikin manyan malaman addninin musulunci a Nijeriya, Sheikh Muhamad Sani Yahaya Jingir, ya yi karin haske akan irin fa'idar dake tattare da Azumin watan Ramadan ga abun da yake cewa a zantawarsu da wakilinmu na Jos Tasiu zakari.11/03/202402:58 -
Saudatu Abubakar kan bikin ranar mata ta duniya
Ranar 8 ga watan Maris din kowacce shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don bikin ranar mata da ke da aniyar lalubo matsalolin da mata ke fuskanta da kuma duba hanyoyin warware su.08/03/202403:31 -
Tattaunawa da Kanal Makiga kan dawowar hare-haren Boko Haram a jihar Borno
A Najeriya rahotanni daga yankin arewa maso gabashin kasar sun nuna yadda mayakan Boko Haram suka koma kai hare-hare bayan lafawar da suka yi, lamarin da ke zuwa kwanaki kalilan bayan rahoton gwamnatin jihar Borno da ya bayyana kawo karshen kaso 95 na masu akidar kungiyar ta Boko Haram.07/03/2024 -
Tattaunawa da Dakta Nazifi Wada Salisu Maigatari kan dambarwar Hisba a Kano
‘Yan Najeriya a ciki da wajen kasar na ci gaba da tattaunawa akan yadda masu shiga tsakani suka sansanta tsakanin gwamnatin Kano da babban kwamandan hukumar Hisba Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa, biyo bayan sabanin da ya kai ga sanarwar yin Murabus da shugaban hukumar yayi.06/03/202403:35 -
Umar Alangawari kan kai wa motocin dakon kayan abinci da rumbuna hari
Batun kai hari tare da daka wawa kan rumbunan ajiyar kayayyakin abinci na hukumomi a wasu yankunan Najeriya na neman zama ruwan dare, la’akari da yadda a ‘yan kwanakin nan hakan ta rika faruwa, yayin da kuma a wasu lokutan aka rika tare motocin dakon abincin tare da afka musu, lamarin da ake alakantawa da tsananin tsadar rayuwa da yunwar da ke addabar dimbin mutane a Najeriya.05/03/202403:19 -
Muhammadu Magaji: Kan yadda Najeriya za ta inganta harkar noma
Masana harkar noma da samar da abinci sun bayyana cewar Najeriya na da duk abinda take bukata wajen ciyar da kan ta muddin ta inganta harkar noman kasar, amma kuma sakaci daga hukumomi da matsalar tsaro na ci gaba da yiwa kasar tarnaki.01/03/202403:25 -
Mu'azu Magaji: Kan dambarwar Hisbah da gwamnatin Kano
Yau al’ummar Jihar Kano dake Najeriya sun tashi da labarin murabus din da shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi daga mukamin sa, sakamakon abinda ya kira sanyaya masa gwuiwar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi, wajen sukar yadda suke gudanar da aikin su.01/03/202403:40 -
Alhaji Mukhtar Hussain kan maido da tsarin bai wa ‘yan canji dala da CBN yayi
Babban Bankin Najeriya ya maido da tsarin bai wa ‘yan canji dala, a wani mataki na farfado da darajar Naira wadda ta fadi warwas a kasuwar hada-hadar kudade. CBN ya ce, zai rika sayar wa masu lasisi dala dubu 20 a kan farashin Naira dubu 1 da 301, yayin da ya shinfida musu wasu ka’idoji da suka hada da cin ribar da ba ta wuce kashi 1 na farashin da ya sayar musu da dalar ba.28/02/202403:07 -
Comrade Nasir Kabir kan zanga-zangar lumanar kungiyar kwadago ta Najeriya
Yau kungiyoyin kwadago a Najeriya ke gudanar da zanga-zangar lumana a kan tsadar rayuwa, sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin kasar tayi, wanda ya haifar da mummunar hauhawan farashin kayan masarufi. Kungiyar NLC ta kira zanga-zangar a biranen kasar wajen ganin gwamnati ta saurari korafe-korafen jama'a dangane da halin kuncin da suka samu kan su.27/02/202403:32 -
Amb Ibrahim Kazaure kan janye takunkumin ECOWAS ga kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso
Kungiyar ECOWAS ta sanar da janye takunkumin karya tattalin arzikin da ta sanyawa kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso, yayin da ta bukaci sojojin da suka yi juyin mulki a wadannan kasashe da su dawo teburin tattaunawa domin samo hanyar mayar da mulkin dimukiradiya a cikin su. Shugabannin ECOWAS sun ce an cire takunkumin ne saboda dalilan jinkai, kuma matakin ya kawo karshen hana zirga zirgar jiragen sama da bude asusun ajiyar wadannan kasashe guda 3.26/02/202403:31
Bakonmu a Yau
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.