Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Yadda tsadar rayuwa ke barzana ga Maroka da Sankira a Jamhuriyar Nijar
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya duba yadda jama'a a Maradi suka koma amfani da ruwan randa a maimakon kankara lokacin azumin watan Ramadana, saboda tsadar kankarar.26/03/202410:09 -
Yadda masarautar Hausawan Turai ke gudanar da ayyukanta
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Sarkin Hausan Turai Alhaji Surajo Jankado Labbo da ke kasar Faransa, inda Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shi kan wasu batutuwa da suka shafi Hausawa.19/03/202410:17 -
Tasirin masu sarautar gargajiya wajen inganta tsaro a yankunansu
A sakamakon gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin Nigeria na 1976, aka tsame hannun sarakunan gargajiya a kasar cikin sha’anin kula da harkokin tsaro da harkokin shari’ah da kuma batun tara haraji a cikin al’ummarsu.Hakan ne ya sanya Sarakuna duk da kasancewarsu iyayen kasa, suka koma gefe inda suka zamo ‘yan kallo kan wadannan al’amura.05/03/202410:02 -
Yadda kananan kabilu suka samu wakilci a masarautar Katsinar Maradi
Shirin Al'adun Gargajiya na wannan makon ya ziyarci masarautar Katsina Maradi da ke Jamhuriyar Nijar, inda Sultan Ahmed Ali Zaki ya fitar da wani tsari na nada kananan kabilu a mukaman wakilan al’ummarsu, don kara dankon zumunci tsakanin kabilu sannan da raya al’adun gargajiya a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.Baya ga Fulani da Bugaje da ke zama 'yan gida, Sultan ya nada wakilan Adarawa, Zabarmawa da Tubawa.27/02/202409:39 -
Shiri na musamman kan marigayi Salissou Hamissou
Shirin "Al'adunmu na gado" a wannan makon na musamman ne, wanda ya yi duba akan irin gudunmuwar da marigayi Salissou Hamissou ya bayar a bangaren al'adu, musamman a lokacin da ya ke gabatar da wannan shiri na Al'adunmu na gado.20/02/202410:51 -
Yadda al'adar auren Zaga ke shudewa tsakanin kabilar Sayawa a Najeriya
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda auren Zaga tsakanin al'ummar Sayawa ke komawa tarihi, salon al'adar da ke bayar da damar gadon mace ko kuma bayar da kyautar ta da sunan aure.13/02/202409:28 -
Yadda wasu abincin gargajiya na bahaushe ke barazanar bacewa
Shirin al'adunmu na gado na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda abinci gargajiya irin na Bahaushe ke bata sannu a hankali12/12/202310:01 -
Yadda sana'ar rini ke bacewa sannu a hankali a arewacin Najeriya
Shirin 'Al'adun Gargajiya' na wannan makon tare da Abdullahi Issa ya maida hankali ne kan bacewar sanar gargajiya ta rini a jihar Kano dake arewacin Najeriya, kafin daga bisa shirin ya leka Maradi dake jamhuriyar Nijar.14/11/202310:19 -
Bikin cika shekara daya da sarkin Katsinar Maradi yayi da hawa kan karagar mulki
Shirin Al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya maida hankali ne kan cika shekara daya da sabon sarkin Katsinar Maradi,Mai Martaba Ahmad Ali Zaki Maremawa yayi kan karagar mulki. A dai ranar Asabar 5 ga watan Nuwambar shekarar da ta gaba ne aka nada Mai Martaba Ali Zaki a matsayin Sultan na 2 na Katsinar Maradi.07/11/202310:48 -
Bafaranshiya ta lashe kyautar iya gasa biredi ta duniya
Shirin Al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya tabo batun kyautar da matashiya 'yan Farsans ta lashe, inda ta zamo ta daya a duniya a wannan shekarar wajen iya gasa biridi. Tarihi dai ya nuna wannan ne karo na faro da mace ta taba lashe wannan kyauta.31/10/202310:31 -
Yadda za'a bunkasa harshen Kanuri da al'adun sa
Shirin al'adunmu na gado na wannan mako ya duba wani babban taron kasa da kasa da aka gudanar kan habbaka harshen Kanuri da al'adunsa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya24/10/202310:14 -
Shekaru 30 na Sarkin Masarautar Zazzau Suleja
Shirin Al'adunmu na wannan mako ya yada zango ne Masarautar Zazzau Suleja ta jihar Neja dake Najeriya domin shaida bikin murnar cika shekaru 30 na Sarkin Masarautar mai dimbin tarihi, Mallam Muhammadu Auwal Ibrahim, wanda ya kasance gwamnan jihar na farko na farar hula a jamhuriya ta biyu daga shekarar alif 979 zuwa alif 983.17/10/202310:00 -
Yadda sauyin zamani ke shirin batar da sana'ar wanzanci
Shirin Al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya yi duba ne kan sana’ar wanzanci, wacce ke cikin sana'oin gargajiya na Hausawa da ke cike da abubuwa na al’ajabi. Mafi yawancin wanzamai gadon sana’ar suke yi daga iyayensu, amma wani lokacin, ana samun wasu daga waje da suke sha’awar koyon sana’ar don su samu hanyar cin abici. Duk kuwa da yadda bincike ya nuna cewa sana’ar ba abar da mutum zai koya cikin sauki da sauri ba ce.10/10/202310:11 -
Yadda harshen Hausa ke samun karbuwa a jami'o'in Burkina Faso
Shirin ala'dun mu na gado na wannan mako zai mayar da hankali ne kan taron inganta harshen Hausa da aka shirya a jami'ar Ouagadougou da ke Burkian Faso26/09/202310:02 -
Bukukuwan al'adun kabilar Dukkawa
Shirin al'adun gargajiya na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda kabilar Dukkawa na jihar Neja da ke tarayyar Najeriya suke gudanar da bukukuwan gargajiya na shekara-shekara.12/09/202310:15
Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.