An sake yin arrangama tsakanin jami'an tsaro da 'yan Shi'a
Akalla ‘ya’yan kungiyar ‘yan uwa Musulmi IMN da aka fi sani da Shi’a guda 6 ne suka rasa rayukansu a Najeriya, ciki har da mataimakin kwashinan 'yan sanda yayin arrangama da da jam’an tsaron a Abuja babban birnin kasar. Wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP ya tabbatar da ganin gawarwakin 6, yayin Karin bayani kan yadda lamarin ya auku a wannan litinin. Bayan isa gaf da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ne, ‘yan sanda suka yi kokarin dakatar da zanga zangar, matakin da ya wani gungu daga cikin ‘yan kungiyar ta ‘yan uwa Musulmi cinnawa ginin hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA da ke kusa wuta, abinda yayi sanadin konewar dukiya da aka kiyasta darajarta ta kai akalla naira miliyan 200.