Isa ga babban shafi
Nijar

Jagoran 'yan adawar Nijar ya koma gida bayan gudun hijirar shekaru 3

Jagoran ‘yan adawar Jamhuriyar Nijar Hama Amadou ya koma gida bayan kwashe shekaru 3 yana gudun hijirar kashin kansa, sakamakon tuhumar da aka masa kan aikata laifin safarar jarirai.

Jagoran yan adawar jamhuriyar Nijar  Hama Amadou.
Jagoran yan adawar jamhuriyar Nijar Hama Amadou. RFI Hausa
Talla

Kotun da ta saurari karar da aka kai shugaban Yan adawan Hama Amadou kan safarar jarirai ta yanke masa hukuncin daurin shekara guda a bayan idan sa, bayan ya fice daga kasar.

A shekarar 2016 shugaban yan adawar ya fice daga Jamhuriyar Nijar zuwa kasar Faransa, inda aka kamala shari’ar da aka masa ba tare da ya gurfana a kotu ba.

Bayan shekaru 3, Hmaa Amadou ya koma gida a cikin wani jirgin saman kasar Cote d’Ivoire da ake kira Air Ivoire, inda ya samu tarba daga Yan uwa da tarin magoya bayan sa.

Tsohon shugaban majalisar dokokin ya ziyarci kabarin mahaifiyar sa da ta rasu a watan jiya, kafin ya isa gidan sa.

Masu sa ido na cewa, ganin irin tarbar da ya samu, akwai alamun cewar Hama zai sake komawa cikin harkokin siyasa kamar yadda ya bayyana wajen wani taro watanni 6 da suak gabata a kasar Ghana da Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.