Isa ga babban shafi
Nijar

'Yan ta'adda sun kashe sojojin Nijar

Ma’aikatar Cikin Gidan Jamhuriyar Nijar ta ce, an kashe sojojin kasar biyu tare da jikkata biyar a wani harin ta’addanci da aka kaddamar a yankin kudu maso yamacin kasar.

Wasu daga cikin sojojin Nijar a cikin shirin ko-ta-kwana
Wasu daga cikin sojojin Nijar a cikin shirin ko-ta-kwana US Army/Richard Bumgardner
Talla

Ma’aikatar Cikin Gidan Nijar ta ce, wata bataliyar jami‘an tsaron kasar ta yi artabu da ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai a kusa da gunzumar Dogon Kiria a ranar Lahadin da ta gabata.

Sanarwar da Ma’aikatar ta fitar ta ce, an fatattaki ‘yan ta’addan bayan zazzafar fafatawar da aka yi da su, sai dai jami’an sojin kasar biyu sun kwanta dama, amma babu alkaluman wadanda suka mutu ko kuma jikkata daga bangaren ‘yan ta’addan.

A karo na biyu kenan da ake kai farmaki a yankin Dogondoutchi duk da cewa, an dauki tsawon lokaci ba tare da jin duriyar ‘yan ta’adda a wannan yanki ba.

A cikin watan Fabairun da ya gabata, an kashe jandarmomi biyu da farar hula guda a harin da ‘yan bindiga suka kai a kauyen Bagaji da ke wannan yanki.

Yankin na Dogondoutchi na kusa da tarayyar Najeriya, amma dai akwai tazarar daruruwan kilomitoci tsakaninsa da yankin Diffa, in da mayakan Boko Haram suka sha kai hare-hare.

Tuni shugaban kasar ta Nijar, Muhammadou Issoufou ya bukaci taimako daga kasashen yammacin duniya da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya domin magance matsalar ta’addanci a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.