Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 23/01 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 23/01 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 23/01 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 23/01 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 23/01 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 23/01 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 23/01 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 22/01 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 22/01 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Nijar

Mahara sun hallaka sojin Nijar 28 a Tongo Tongo

media Wasu dakarun rundunar sojin Jamhuriyar Nijar. Autre presse par DR

Gwamnatin Nijar ta ware tsawon kwanaki uku daga yau Alhamis domin alhinin mutuwar sojojin kasar 28 sakamakon harin ta’addaanci da aka kai ranar talatar da ta gabata.

Da farko dai majiyoyin tsaro sun bayyana cewa sojoji 17 ne suka rasa rayukansu yayin da 11 suka bata, to amma daga bisani an bayyana su ma sun rasa rayukansu a wannan hari da ya faru a Baley Beri kusa da iyakar kasar da Mali.

Motoci 8 na bataliyar sojojin kundumbala mai 112 da ke da babbar cibiyarsu a garin Walam ne aka kai wa wannan hari na kwanton bauna, a wani wuri mai tazarar kilomita 45 a arewacin garin Mangaize, kusa da kauyen Tongo-Tongo gaf da iyakar kasar ta Nijar da Mali.

A jimilce sojoji 52 ne ke cikin wannan ayari da ke kokarin murkushe ‘yan ta’addar da suka kai hari a gidan yarin Kuti-Kale, inda daya daga cikin motocin sojin ta taka nakiya.

Bayan fashewar nakiyar, nan take ‘yan ta’addar suka bude wa sojojin wuta, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar 17 daga cikinsu, daya ya samu rauni yayin da har yanzu ake ci gaba da neman wasu 11.

Bayanai sun ce jim kadan bayan faruwar harin, an ga jiragen yaki guda uku, daya na Nijar, daya na Faransa da kuma daya na Amurka na shawagi a kusa da inda lamarin ya faru, to sai dai wasu majiyoyi sun ce wadannan jirage sun dawo sansaninsu da ke Yamai ba tare da sun yi nasarar kama ko da daya daga cikin ‘yan ta’addar ba.

Ga alama dai ba daya daga cikin wadannan ‘yan ta’adda da ya tsallaka iyakar kasar ta Nijar zuwa Mali, yayin da wata majiya ke cewa sun samu mafaka ne a cikin al’ummar da ke rayuwa a kauyukan da ke wannan yanki.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure