Isa ga babban shafi
Nijar

Sojin Nijar sun kashe 'yan Boko Haram kusan 300

Dakarun Jamhuriyar Nijar sun kashe mayakan Boko Haram 280 a wasu jerin hare-hare da suka hada da luguden wuta ta sama da suka kaddamar musu kamar yadda Ma’aikatar Tsaron kasar ta sanar.

Sojin Nijar a Bosso
Sojin Nijar a Bosso ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar Tsaron Nijar ta ce, an kashe mayakan ne a wani aikin kakkabe su da aka fara gudanarwa a ranar Jumma’ar da ta gabata a kusa da kogin Komadugu da ya raba Nijar da Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewa, an kuma raba mayakan na Boko Haram sama da 200 da makamansu.

Kungiyar Boko Haram ta shafe tsawon shekaru tana kaddamar da farmaki kan kasashen Nijar da Najeriya da Chadi da Kamaru, yayin da a cikin watan Yulin shekarar 2016, ta kashe sojojin Nijar fiye da 30 a garin Bosso, abin da ya sa Chadi ta aika da sojoji dubu 2 don taimakawa kasar a wannan yaki.

Ko da yake a cikin watan Oktoban 2017 ne, Chadi ta janye wadannan dakaru, abin da ya haifar da dari-dari kan makomar tsaro a yankin Diffa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.