Isa ga babban shafi
Nijar-Algeria

Algeria ta sake tasa keyar 'yan Nijar zuwa Agadez

Duk da kokarin da hukumomin Jamhuriyar Nijar keyi na hana ‘yan kasar tafiya kasashen waje domin yin bara ganin yadda ake cin zarafin su, matsalar na ci gaba da karuwa.

Wasu 'yan gudun hijira akan iyakar Algeria da Nijar.
Wasu 'yan gudun hijira akan iyakar Algeria da Nijar. NBC News/IOM
Talla

Rahotanni daga Nijar sun ce ko a karshen makon da ya kare, hukumomin Algeria sun sake tasa keyar wasu ‘yan kasar sama da 100 zuwa birnin Agadez.

Wakilinmu a garin Agadez Omar Sani ya aiko da rahoto akai.

01:25

Algeria ta sake tasa keyar 'yan Nijar zuwa Agadez

Oumarou Sani

Ci gaba da tasa keyar bakin-haure daga Nijar da sauran kasashe da Algeria ke yi, na zuwa a dai dai lokacin da majalisar dinkin duniya ta bukaci gwamnatin kasar ta dakatar da matakin.

Majalisar ta kuma bukaci inganta kular da jami’an tsaron Algeria ke baiwa bakin dake tsare a hannunsu daga kasashen Mali da Nijar, wadanda ta ce mafi akasarinsu suna tsare ne cikin muhalli maras kyawun yanayi.

Zuwa yanzu dai Algeria, wadda ke da iyaka mai nisan akalla kilo mita  2,500 da kasashen Mali da Nijar, ta kashe kimanin dala miliyan $20 cikin shekaru uku da suka gabata, domin magance matsalolin da kwararar bakin-haure ke haddasa mata, da kuma kula da su wadanda ke tserewa yaki, da sauran matsalolin tsaro da kuma talauci a yankin Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.