kungiyoyin farar hula sun taka muhimmiyar rawa wajen shimfiduwar demokradiya a Nijar
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:27
Yayin da ake cigaba da takun saka tsakanin gwamnat da kuma ‘yan adawa a Jamhuriyar Nijar dangane da batun yi wa dokokin zabe na kasar gyaran fuska, kungiyoyin fararen hula wadanda suka taka gagarumar rawa domin shimfida tsarin dimokuradiyya a kasar, sun bukaci ‘yan siyasar da su mayar da hankali kan makomar kasar a maimakon kare muradunsu na siyasa kawai.Alhaji Moustapha Kadi, daya daga cikin wadanda suka taka gagarumar rawa domin kafa gungun CNDP da ke sulhunta rikicin siyasa, ya ce bai kamata a manta da irin rawar da kungiyoyin fararen hular suka taka wajen girka dimokuradiyya a kasar ta Nijar ba.