Mace ta farko da ta fara aikin jarida a Nijar ta rasu
Mace ta farko da ta fara aikin jarida a Jamhuriyar Nijar, Mariam Keita ta rasu tana da shekaru 72 a duniya, bayan tayi fama da rashin lafiya.
Wallafawa ranar:
Wani na kusa da 'yar jaridar Ibrahim Moussa ne ya sanar da labarin rasuwarta, yayin da kafofin yada labaran kasar suka yada shi.
An dai haifi Mariama Keita a shekarar 1946 cikin Birnin Yammai, kuma itace Daraktar farko ta tashar Radiyo Sahel, mallakar gwamnati a matsayin Edita da kuma mai gabatar da labarai.
Tsakanin shekarar 2003 zuwa 2006 ta zama shugabar Majalisar Sadarwar gwamnati da dake sa ido kan harkar sadarwa a Nijar.
Keita na daga cikin Yan kungiyoyin fararen hula da kungiyar mata, wadda ta taka rawa wajen fadakar da jama’a kan fahimtar kundin tsarin mulki da y abada damar gudanar da zaben dimokiradiya na farko a shekarar 1993.
Mutuwar na ta na zuwa ne kwanaki bayan mutuwar Amadou Ousmane, tsohon Darakan Hukumar yada labarai kuma mawallafin kan matsalar cin hanci a kasashen Afirka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu