Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Ministan lafiyan Nijar Dakta Ilyassou Idi Mainassara kan korar jami'ar lafiya da ta wallafa bayanan karya

Wallafawa ranar:

Mahukunta a Jamhuriyar Nijar sun kori wata jami’ar kiwon lafiya da ke aiki da Kungiyar Medecins Sans Frontieres daga kasar, sakamakon wallafa alkaluman karya da ke cewa ana samun mutuwar yara kanana akalla 10 sakamakon zazzabin cizon sauro da kuma rashin abinci mai gina jiki a yankin Maragaria da ke Damagaram.Bayan fitar da wadannan alkalumma da jami’ar mai suna Anne Pittet ta wallafa a wani hoton bidiyo, ministan kiwon lafiyar kasar da kuma shugaban ofishin MSF a Nijar sun yi tattaki har zuwa Maragaria, domin sanin inda ta samu wadannan alkalumma.Ministan lafiya na kasar Dr Ilyassou Idi Mainassara, ya yi karin bayani a game da matakin da suka dauka kan jami’ar kiwon lafiyar, a tataunawarsa da AbdoulKareem Ibrahim Shikal.

Mahukunta a Jamhuriyar Nijar sun kori wata jami’ar kiwon lafiya da ke aiki da Kungiyar Medecins Sans Frontieres, sakamakon wallafa alkaluman karya.
Mahukunta a Jamhuriyar Nijar sun kori wata jami’ar kiwon lafiya da ke aiki da Kungiyar Medecins Sans Frontieres, sakamakon wallafa alkaluman karya. AFP
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.