Kotu ta bada umarnin bude gidan rediyon Nijar
Wata Kotu a Jamhuriyar Nijar ta bada umurnin bude gidan rediyon Labari da gwamnati ta rufe a karshen mako saboda zargin cewar yana tinzira jama’a wajen tada hankali.
Wallafawa ranar:
Alkalin kotun ya bayyana matakin rufe tashar a matsayin abin da ya saba ka’ida, in da ya bukaci jami’an tsaron da suke girke a tashar da su san in da dare ya yi musu.
Ali Idrissa, daya daga cikin shugabannin da suka shirya zanga zangar adawa da harajin gwamnati na can tsare a gidan yari tare da sauran abokan tafiyarsa.
Ministan cikin gida, Bazum Muhammed ya zargi tashar da zama bakin 'yan adawa wajen tinzira al’ummar kasar su yi mata bore.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu