Yayin da yake karin haske kan shirin, Ministan kudin Nijar Hassoumi Massaoudou, ya ce tattaunawar zata kuma duba yi wuwar karkata akalar shinfida bututun man zuwa tshar ruwa dake birnin Kwatano idan aka cigaba da fuskantar barazanar tsaro daga mayakan Boko Haram a Kamaru.
Tun shekara ta 2013 ne ake tattaunawa kan wannan shiri, sai dai bullar ‘yan Boko Haram ya haifar da cikas.