Isa ga babban shafi
Nijar

Tushen abinda ya auku a Nijar kan kisan sojin Amurka

Wasu majiyoyi daga Amurka sun ce bayanan da kwamandodin sojin kasar suka gabatar kan yadda dakarunsu 4 suka mutu a Nijar ya sabawa asalin abinda ya faru.

Wasu sojin kasar Nijar yayinda suke sintiri a kan iyakar kasar da Najeriya yankin  Diffa, Niger.
Wasu sojin kasar Nijar yayinda suke sintiri a kan iyakar kasar da Najeriya yankin Diffa, Niger. REUTERS/Luc Gnago.
Talla

Bayanan baya bayan nan sun nuna cewar, dakarun sun je inda aka samu hadarin ne domin kama wani kwamandan ‘yan ta’adda da ake kira Dandou cikin dare.

Bayan kashe sojojin Amurka guda 4 Babban Hafsan Hafsoshin Amurka, Janar Joseph Danford yace sojojin sun je yankin na Nijar ne domin sanya ido kan halin da ake ciki.

Janar Dunford yace sojojin Amurka 12, na tawagar tare da sojojin Nijar 30, lokacin da ‘yan tawayen 50 dake da alaka da kungiyar IS suka kai musu hari a Tongo Tongo.

Hafsan yace sojojin sun dauka zasu iya murkushe maharan ne ya sa basu nemi akai musu dauki ba.

Sai dai wata majiyar leken asirin Amurka ta shaidawa tashar ABC cewar, sojojin sun kai samame ne cikin dare, domin kama wani shugaban ‘yan ta’adda da ake kira Dandou ko kuma hallaka shi.

Majiyar tace dadewar da suka yi a yankin ya sa aka gane su aka kuma kai musu hari.

Tashar ABC ta ruwaito wani jami’in Nijar na cewa, sojojin su nemi akai musu dauki lokacin da aka kai musu hari, amma kuma kwamnadodin Amurka suka ki.

ABC ta nemi Karin haske daga ma’aikatar tsaron Amurka amma sun ki cewa komai kan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.