Isa ga babban shafi
Nijar

Fararen hula sun soki hukuncin kotu kan 'ya'yan Hama Amadou

Kungiyoyin fararen hula a Nijar sun bayyana shakkunsu dangane da makomar yara 16 da aka bayyana cewa an sayo su ne daga waje, wadda kotu ta bayar da umurnin damka su a karkashin kulawar gidajen marayu.

Tsohon shugaban majalisar dokokin Nijar Hama Amadou
Tsohon shugaban majalisar dokokin Nijar Hama Amadou ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Daga cikin wadannan yara har da wadanda kotu ta samu tsohon shugaban majalisar dokokin kasar Hama Amadou da matarsa da laifin sayowa daga wata kasa ta ketare.

Sai dai Moussa Sidikku na kungiyar kare hakkin kananan yara kanana a Nijar, na ganin cewa wasu daga cikin gidajen marayun ba za su iya bayar da tarbiyar da ake bukata ga wadannan yara ba.

Sidikku ya ce kungiyarsu ta yi Allah-wadai da yadda wasu daga cikin gidajen marayun ke lura da yara.

Ya kuma kara da cewa gidajen ba su da kwarewa da kuma akida mai kyau wanda za a iya cewa sun can-canci a ba su nauyin kula da wadannan yara.

Sai dai ya ce kungiyar tasu ba za ta ja da hukuncin da kotu ta yanke ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.