Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar: Sama da dabbobi 16,000 sun salwanta a ambaliyar ruwa

Ofishin bada agajin jinkai na majalisar dinkin duniya OCHA, ya ce akalla mutane 54 ne suka rasa rayukansu, sakamakon iftila’in ambaliyar ruwan da aka samu a Jamhuriyar Nijar, yayinda sama da mutane 200,000 suka rasa matsugunnasu.

Ambaliyar ruwa a Nijar ta raba dubban mutane da gidajensu.
Ambaliyar ruwa a Nijar ta raba dubban mutane da gidajensu. RFIHAUSA/Awwal
Talla

Ofishin majalisar dinkin duniyar ya kuma ce, mafi akasarin hasarar rayukan ya auku ne birnin Yamai, kuma a birnin kadai akalla gidaje 11,000 ne ambaliyar ruwan ta rusa.

Ofishin bada agajin jikkan na OCHA ya ce Ambaliyar ruwa ta kuma lalata fadin akalla kadada 12,000 na amfanin gona bayaga dabbobi 16,000 da suka salwanta.

Ambaliyar dai ta fi shafar Yamai, Dosso, Tllaberi, Maradi da kuma Zandar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.