Nijar
Djibo-'Yan adawar Nijar za su daukaka kara
Lauyan da ke kare shuagban 'yan adawar Nijar El Hadj Amadou Djibo da aka yi wa daurin talala saboda samun sa da laifin tinzira jama’a don tada hargizi ya ce, za su daukaka kara.
Wallafawa ranar:
Talla
Maître Douleur Oumarou ya bayyana hukuncin a matsayin yunkurin rufe bakin 'yan adawa saboda haka ya ce, za su daukaka kara kan hukuncin.
A watan jiya ne jami’an tsaro suka kama shugaban 'yan adawar bayan ya yi kira ga abokan gwagwarmayarsa da su jajirce domin ganin sun raba shugaban kasar Muhammadou Issofou da karagar mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu