Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar ta sauya wa minista kujera saboda dalibai

Shugaban Jamhuriyar Nijar Issoofou Mahamadou ya sauya wa ministan ilimi mai zurfi na kasar Mohamed Ben Omar kujera, in da ya mayar da shi Minista a ma’aikatar kwadago don kwantar da hankulan dalibai da ke ci gaba da kaurace wa daukar darasi tun ranar Litinin ta makon jiya. 

Shugaban Jamhuriyar Nijar  Issoufou Mahamadou
Shugaban Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou
Talla

A yanzu dai an mika ragamar tafiyar da ma’aikatar ilimin ne a hannun Yahuza Sadisu Madobi, wanda kafin nan ke rike da mukamin ministan kwadago na kasar.

Daya daga cikin sharuddan da daliban suka gindaya wa gwamnati kafin komawa makarantunsu, akwai batun tube ministan na ilimi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne hokumomin Nijar suka ce, an kama jami’an ‘yan sanda uku bayan an zarge su da cin zarafin dalibai masu zanga-zanga, in da mutun guda ya rasa ransa, abin da ya tilasta rufe babban jami’ar kasar da ke birnin Yamai.

Sai dai daga bisani an bude jami'ar ta Abdou Moumouni bayan shugaba Issoufou ya tattauna da shugabannin dalibai don kawo karshen hatsaniyar.

Daliban dai na bukatar gwamnati ta inganta dakunan kwanansu da kuma yanayin gudanar da karatunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.