Gwamnatin Nijar ta rufe dakunan kwanan dalibai

Gwamantin Nijar ta sanar da rufe dakunan kwanan dalibai a babbar jami’ar kasar da ke birnin Yamai. Ministan ilimi mai zurfi na kasar Mohamed Ben Omar ne ya tabbatar da hakan bayan wata kazamar tarzomar da daliban suka yi a jiya Litinin, in da rahotanni ke cewa an raunata daliban da dama, yayin da aka cafke wasu daga cikinsu.Wakiliyarmu a birnin Yamai Lydia Addo na dauke da karin bayani a wannan rahoto.