Kotu a Nijar ta sallami mutane 15 dake tsare don yunkurin juyin mulki na 2015
Wata kotu a kasar Janhuriyar Nijar ta sallami wasu fararen hula 15 da ake tsare dasu bisa zargin hannu a yunkurin kifar da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Isufu a shekara ta 2015.
Wallafawa ranar:
Lauyan mutanen Ali Kadir ya tabbatar da sakin mutann da yake karewa.
A watan 12 na shekara ta 2015 ne dai Gwamnatin Muhammadu Isufu ta sanar da cewa ta yi nasarar hana juyin mulki, kuma tana tsare da wasu mutane dake da hannu a ciki.
Majiyoyin samun labarai na cewa an sallami mutane 15, amma kuma akwai manyan sojoji 9 da suka hada da jagoran kifar da Gwamnatin Janar Salou Souleymane wadanda har yanzu ake tsare dasu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu