Isa ga babban shafi
Nijar

Faransa za ta tura Gwanayen yaki da ta'addanci zuwa kasar Nijar

Faransa za ta aikewa kasar Nijar kwararru ta fannin yakar ta'addanci domin taimakawa Sojan Nijar sakamakon harin da aka kai wa Sojan makon  jiya inda aka kashe masu Dakaru 16.

Shugaban Jamhuriyyar Nijar Issoufou Mahamadou tare da Shugaban Faransa Francois Hollande yayin wata a ziyara a Paris.
Shugaban Jamhuriyyar Nijar Issoufou Mahamadou tare da Shugaban Faransa Francois Hollande yayin wata a ziyara a Paris. REUTERS/Thibault Camus/Pool
Talla

Ma'aikatar Tsaro a Yammai ta sanar cewa matakin na biyo bayan bukata ce da Shugaban Nijar Mahammadou Issoufou ya gabatar wa Faransa.

An kai wannan kazamin hari ne a kusa da kan iyakan Nijar da kasar Mali.

Bayanai na cewa Shugaban Nijar ta tattauna da Ministan Tsaro na Faransa Jean-Yves Le Drian kuma Faransa ta ga dacewar kai daukin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.