Isa ga babban shafi
Nijar

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 50 a Nijar

Akalla mutane 50 ne suka rasa rayukansu yayin da sama da dubu 120 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta shafi yankuna da dama na Jamhuriyar Nijar daga watan Yunin da ya gabata zuwa yau.

Ambaliyar ta hallaka mutane da dama a jamhuriyar Nijar a cikin wannan shekarar
Ambaliyar ta hallaka mutane da dama a jamhuriyar Nijar a cikin wannan shekarar Reuters/路透社
Talla

Rahotan da ofishin hukumar kula da ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya Ocha da ke birnin Yamai ya fitar, na nuni da cewa ambaliyar ta fi tsananta ne musamman a arewacin kasar da ke cikin Sahara, wanda ba kasafai ake samun ruwan sama ba, in da a jumulce aka samu asarar rayukan mutane sama da 50.

Rahoton ya ce, iyalai dubu 16 da 370 ne matsalar ta shafa, in da mutane dubu 123 da 239 suka rasa gidajensu sanadiyyar ambaliyar.

Alkaluman na Majalisar Dinkin Duniya da kuma na gwamnatin Jamhuriyar Nijar sun bayyana yankin Maradi da Tawa da kuma Agadez, su ne suka fi fuskantar ambaliyar ta bana, in da ko baya ga mutane, aka samu asarar dabbobi sama da dubu 20 da suka hada da shanu da awaki da raguna da kuma rakuma.

Har ila yau, ruwan saman da aka sama daga watan na Yuni zuwa yau, ya yi sanadiyyar lalacewar gonaki masu tarin yawa a wadannan yankuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.