Isa ga babban shafi
Nijar

Kasar Amurka tana gina filin jiragen saman yaki a Agadez

Kasar Amurka na ci gaba da gina wani katafaren filin jiragen saman yaki a garin Agedez da ke arewacin jamhuriyar Nijar, sansanin da Amurka za ta yi amfani da shi domin jibge sojojinta. 

Talla

Bayanai daga majiyoyin tsaro a kasar sun ce ginin filin jirgin zai lashe kudi dalar Amurka Miliyan 100, kuma daya ne daga cikin shirye shirye da suka shafi sha’anin tsaro a Jamhuriyyar Nijar.

Tun da jimawa ne dai sojojin Amurka suka shiga kasar ta Nijar, inda suke bayar da horo ga sojin kasar, da kuma amfani da jirage marasa matuki samfurin MQ-9 Reaper domin tara bayanan sirri.

Kakakin ma’aikatar tsaron Amurka Michelle Baldanza ta tabbatar da cewa kasar na ginin filin jirgen saman yaki da Amurkan ke yi a Agadez.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.