Isa ga babban shafi
niger

Za a ninka agajin abinci ga 'yan gudun hijira a Nijar

Majalisar dinkin duniya ta ce, za a ninka agajin abincin da ake bai wa mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu a jamhuriyar Nijar bayan harin baya bayan nan da ya tilasta wa mutane kusan dubu 50 kaurace wa muhallansu.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijira a Nijar
Wasu daga cikin 'yan gudun hijira a Nijar AFP PHOTO/FAROUK BATICHE
Talla

Mataimakin daraktan hukumar samar da abinci ta majalisar da ke kula da jamhuriyar Nijar, Belkacem Machane ya ce, mutanen da suka tsere daga Bosso sun yi tafiyar kilomita 10 zuwa 40 don tsira da rayukansu, kuma yanzu haka suna bukatar abinci da ruwan sha da kuma muhalli.

Jami’in ya ce, ya zama wajibi hukumar ta rubanya abincin da take samarwa don ganin an tallafa wa wadannan mutane da suka bar muhallinsu.

Majalisar na shirin rage adadin abincin da take kuma baiwa 'yan gudun hijirar da ke Diffa wadanda yawansu ya kai dubu 450.

Machane ya ce, yanzu haka babbar kalubalen da ke gabansu shi ne, rashin isashen kudi don tallafa wa wadannan mutane da yanzu haka, ko matsugunin kirki basu da shi, sannan wasu ma a bakin hanya suke zama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.