Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar ta ware kwanakin juyayin mutuwar Alhazai

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ware kwanaki uku daga yau litinin domin juyayin mutuwar ‘yan kasar 22 a turmutsitsin da aka sama ranar alhamis da ta gabata a lokacin aikin hajji.

Mahajjata 22 ne daga Jamhuriyar Nijar aka tabbatar da mutuwarsu a tirmutsitsin da ya auku a Saudiya
Mahajjata 22 ne daga Jamhuriyar Nijar aka tabbatar da mutuwarsu a tirmutsitsin da ya auku a Saudiya REUTERS
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya jiyo Ministan shari’a kuma kakakin gwamnatin kasar Morou Amadou ya ce, ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu akwai wasu mutane da dama da suka bata.

A jumulce dai, hukumomin Kasar Saudiya sun tabbatar da mutuwar Mahajjata 769 cikin kimanin Miliyan 2 da suka isa Kasar daga sassan duniya domin aikin hajji na bana, kuma 'Yan Kasar Iran ne hadarin ya fi ritsawa da su, inda Alhazan Kasar 144 suka rigamu gidan gaskiya.

Sai kuma Kasar Morocco dake biye mata wadda ta rasa Mahajjatanta 87.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.