Abuba Albade zai iya magana da sunan MNSD Nassara
Kotu a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, ta cire haramcin da wata kotun ta sanya wa reshen jam’iyyar adawa ta MNSD Nasara da ke karkashin jagorancin Abuba Albade, wanda a can baya aka umurce shi da ya daina yin Magana da sunan jam’iyyar.
Wallafawa ranar:
Ana ci gaba da fuskantar tsaiko a Jamhuriyar ta Nijar yayi da wasu daga cikin yan siyasa ke ci gaba da zargin Gwamnatin Shugaba Mahamadou Issifou da neman wargaza jam'iyyoyin siyasar wannan kasar.
A dai wajen kotun ta ce Albade Abuba zai iya ci gaba da yin Magana da sunan jam’iyyar MNSD Nassara, sai zuwa ranar 7 ga watan satumba lokacin da kotun za ta yanke hukuncin karshe. Alhaji Ibro Ayuba, daya daga cikin na hannun damar Albade, ya bayyana gamsuwarsu da wannan hukunci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu