Nijar
An Kaddamar da aikin layin dogo daga Nijar zuwa Cotonou
Shugaban kasar Nijar Muhammadou Issofou ya jagoranci bikin fara aikin gina layin dogo na jirgin kasa da zai tashi daga Yammai zuwa Cotonou da kuma Yammai zuwa Abidjan a lokacin da gwamnatinsa ke bikin cika shekaru uku. Bikin ya samu halartar daruruwan mutane cikin su har da shugaban Jamhuriyar Benin Bonni Yayi da Faure Gnassingbe na Togo, da kuma wakilan gwamnatin Najeriya da Cote d'Ivoire. Bashir Ibrahim Idris da ya halarci bikin ya aikon da Rahoto daga birnin Yamai.
Wallafawa ranar:
Talla
Rahoto: Gwamnatin Issoufou ta cika shekaru uku
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu