Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojan Najeriya ya kashe abokan aikinsa a Borno

Rundunar Sojin Najeriya ta ce, wani sojinta da ke aiki a karkashin rundunar da ke yaki da Boko Haram a Malam Fatori na Jihar Barno, ya harbe wasu abokan aikinsa guda 4 har lahira da kuma raunata wasu guda 2 kafin daga bisani ya kashe kansa.

Wasu daga cikin sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram
Wasu daga cikin sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram Pulse.ng
Talla

Daraktan Yada Labaran Sojin, Kanar Sagir Musa ya tabbatar da aukuwar lamarin, yayin da ya ce hukumomin soji na kokarin tintibar 'yan uwan wadanda hadarin ya ritsa da su.

Kanar Musa ya ce, tuni aka kaddamar da bincike kan lamarin domin gano dalilin aikata wannan aika-aikar.

Sojin Najeriya sun kwashe sama da shekaru 10 suna yaki da mayakan Boko Haram wadanda ke amfani da muggan makamai wajen kai hare-hare a birane da kauyukan da ke arewa maso gabashin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.