Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta cilla karamin yaro cikin mota mai ci da wuta

Tsohon gwamnan jihar Lagos a mulkin soji, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya ce, ya samu bayanai kan cewa, mayakan Boko Haram sun cilla wani karamin yaro cikin wata mota da ke kan ganiyar ci da wuta a yayin harin da suka kaddamar a garin Auno na jihar Borno makwanni biyu da suka gabata.

Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya ziyarci Auno bayan harin Boko Haram da ya kashe kimanin mutane 30
Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya ziyarci Auno bayan harin Boko Haram da ya kashe kimanin mutane 30 TheCable
Talla

Mawrwa ya bayyana haka ne a yayin zantawa da kafar talabijin ta Channels a ranar Litinin, inda ya ce, mutumin da ya kwankwadi muggan kwayoyi ne kadai zi iya aikata wannan mummunan aikin.

Wata mata ce da ke cikin motar mai ci da wuta, ta cillo danta waje da nufin tsirar da shi, amma mayakan na Boko Haram suka mayar da yaron cikin motar don shi ma ya babbake tare da mahaifiyarsa.

Rahotanni sun ce, a kalla mutane 30 suka rasa rayukansu a yayin wannan kazamin farmakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.