Ku bamu miliyan 1 ko mu kai muku hari- 'Yan bindigar Katsina
Rahotanni daga jihar Katsina ta Najeriya sun ce, wasu ‘yan bindiga sun bukaci mazauna kauyen Akate da ke Karamar Hukumar Batsari da su biya Naira miliyan 1 domin kauce wa fuskantar hare-haren ‘yan bindigar.
Wallafawa ranar:
Majiyoyin sirri sun ce, tuni mazauna kauyen suka fara karbar Naira dubu 1 da 500 daga kowanne mutun guda domin tara kudaden da ‘yan bindigar suka bukata.
Kauyen Akate na cikin wuraren da ba su da karfin kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga a Katsina.
Ko a makwanni biyu da suka shude, sai da ‘yan bindigar suka dirar wa kauyen, inda suka sace tarin dabbobi.
Wasu daga cikin mazauna kauyen sun yi nasarar kwato dabbobinsu bayan sun fatattaki daya daga cikin barayin, sannan suka mika shi ga sojoji.
Wannan al’amarin ne ya fusata ‘yan bindigar har suka nemi mazauna kauyen da su tara musu Naira miliyan 1 domin kauce wa fuskantar farmakinsu.
Kodayake wasu bayanai sun ce, daga bisani ‘yan bindigar sun amince a biya su Naira dubu 700 bayan sun cimma yarjejeniyar rangwame da mazauna kauyen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu