Isa ga babban shafi

Boko Haram ta kai munanan hare hare a kauyukan Chibok

Mayakan Kungiyar Boko Haram sun kaddamar da munanan hare hare a kauyukan Chibok dake Jihar Barnon Najeriya inda suka kona gidaje da kuma satar abinci.

Sojojin Najeriya kan hanyar Chibok a arewacin Borno
Sojojin Najeriya kan hanyar Chibok a arewacin Borno AFP PHOTO/SUNDAY AGHAEZE
Talla

Rahotanni sun ce mayakan sun kai harin ne da maraicen Talata a kauyen Korongilum a motocin yaki da babura da yamma lokacin da mazauna yankin ke komawa gidajen su daga harkoin yau da kullum.

Daya daga cikin shugabannin al’ummar yankin Hosea Tsimbido yace yayin da suke kai harin mazauna kauyen sun samu labari inda wasu daga cikin su suka tsere, abinda ya sa suka tsira da rayukan su.

Tsinbido yace lokacin kai harin sun yi arangama da sojoji da kuma matasan JTF inda suka kashe wasu daga cikin su, kana suka dauki motar su.

Shugaban al’ummar yace mayakan sun kona gidaje da dama bayan sun kwashe kayan abinci sun yi gaba da shi.

Ya zuwa yanzu rundunar sojin Najeriya ba tace komai ba dangane da harin, amma a cikin 'yan kwanakin nan mayakan Boko Haram na kai hari jifa jifa a yankunan Jihar Barno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.