Isa ga babban shafi
Najeriya

NFF ta baiwa Amokachi shugabancin kula da koca-kocai

HUKUMAR Kwallon kafar Najeriya ta sanar da nada tsohon tauraron kwallon kafar kasar Daniel Amokachi a matsayin shugaban sashen kula da  koca-kocai da ake kira da turanci ‘Technical Department’.

Nigeria Footbal Federation Appoints Amokachi Technical Adviser
Nigeria Footbal Federation Appoints Amokachi Technical Adviser CEOAfrica
Talla

Hukumar tace Amokachi ya samu nasarar ce bayan fafatawar da yayi da wasu fitattun kwachochi irin su Mike Emenalo da yayi aiki da kungiyar PSG da Chelsea da Austin Eguavoen da ya jagorancin Super Eagles da Ladan Bosso da Sam Okpodu da kuma Mutiu Adepoju.

Amokaci wanda ya taba zama mataimakin Stephen Keshi wajen jagorancin Super Eagles zai gaji Bitrus Bewarang wanda ya kamala wa’adin aikin sa.

Tsohon tauraron dan was an Najeriya Amokachi ya bugawa kungiyoyi da dama da suka hada da Ranchers ta Kaduna kafin ya tafi kasar Belgium inda ya yiwa Clubb Brugge wasa kafin ya koma Everton dake England inda ya lashe kofin kalubalen kasar.

Amokachi ya kuma yiwa Besiktas ta turkiya da Colorado Rapids dake Amurka wasa, kafin ya karkare a Nasarawa United.

Yayi kuma aiki a matsayin mai horar da Yan wasan Nasarawa United da Enyimba kafin ya koma Super Eagles domin taimakawa Stephen Keshi.

Amokaci na daga cikin Yan was an Najeriya da suka lashe kofin zinare na Olympics a shekarar 1996 da kuma kai Najeriya cin kofin duniya na manya a karon farko a 1994.

A makon jiya shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Amokachi a matsayin Jakadan kasar kan harkokin kwallon kafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.