Isa ga babban shafi
Najeriya

Ba za mu iya korar hafsoshin tsaron Najeriya ba-Fadar Buhari

Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa, ba za ta iya sallamar manyan hafsoshin tsaron kasar ba a yanzu, tana mai cewa, lokacin korar su bai yi ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da manyan hafsoshin tsaron kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da manyan hafsoshin tsaron kasar. Punch
Talla

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya bayyana haka a babban birnin Abuja a yayin kaddamar da wani littafi.

‘Yan jaridu ne suka yi wa sakataren gwamnatin tambaya game da manyan hafsoshin tsaron da wasu ke korafin cewa, sun gaza samar da tsaro a kasar baya ga kuma jimawar da suka yi suna rike fda madafun iko.

A cewar Boss “ Ba haka kawai ake korar mutane ba, akwai hanyoyi kuma na yi amanna cewa,idan lokaci ya yi, za a bi hanyoyin”.

Da dama daga cikin 'yan Najeriya na cewa, hafsoshin tsaron sun gaza magance rikicin Boko Haram da ke addabar yankin arewa maso gabashin kasar, ga kuma matsalar 'yan bindiga da sace-sacen jama'a da ke ci gaba da ta'azzara a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.