Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Najeriya ba su san suna dauke da cutar Koda ba

Wata kungiyar likitoci a Najeriya ta ce, al’ummar kasar miliyan 20 ke dauke da cutar ciwon koda, kuma akasarinsu ba su san cewa suna dauke da cutar ba.

Mutane miliyan 20 na dauke da cutar Koda a Najeriya
Mutane miliyan 20 na dauke da cutar Koda a Najeriya Centers for Disease Control and Prevention
Talla

Shugabar Kungiyar Frafesa Ifeoma Ulasi ta bayyana haka wajen bude taron kungiyar a garin Ibadan, inda take cewa akwai hanyoyin kamuwa da cutar da dama wanda ya dace ace an yi wa hukumar kula da harkokin lafiya ta kasa garambawul domin fuskantar wadannan matsaloli.

Farfesa Ifeoma ta ce, adadin mutanen da ke dauke da cutar na iya wuce kashi 12 na al’ummar Najeriya, wato sama da mutane miliyan 20.

Shugabar kungiyar ta ce,  wadannan mutane da basu san suna dauke da cutar ba, kan rika zirga zirga zuwa wajen likitocin gargajiya da kuma masu bada maganin karya ba tare da gano abin da ke damun su ba.

Farfesa Ulasi ta bukaci sanya masu fama da cutar koda cikin wadanda za a rika kula da su a karkashin shirin inshoran lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.