Isa ga babban shafi
Najeriya

Burutai ya nanata ikirarin murkushe mayakan Boko Haram

Babban hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Burutai, ya jadadda cewar, babu wani yanki dake karkashin mayakan Boko Haram, biyo bayan murkushe karfinsu da dakarun kasar suka yi.

Babban Hafsan rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai.
Babban Hafsan rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai. AFP PHOTO/STRINGER
Talla

Burutai ya ce hare-haren mayakan na baya bayan ta hanyar harbi ka ruga ba komai bane face yunkurin nuna cewa karfinsu na farfadowa.

Babban Hafsan sojin Najeriyar ya bayyana haka ne, yayin wata zantawa ta musamman cikin karshen mako da kafafen yada labaran ARISE, TheCable, da kuma THISDAY.

Laftanar Janar Burutai ya kuma nanata ikirarinsa na cewar akwai mayakan Boko Haram da dama dake boye cikin jama’ar gari a kauyuka, abinda ke basu damar kai harin “Sari ka Noke” gami da yada farfaganda.

Shugaban rundunar sojin Najeriyar, wanda ya ce yakin da masu tada kayar bayan na tattare da sarkakiya, ya bayyana rashin kyawun hanyoyi zuwa wasu kananan hukumomin jihar Borno a matsayin wasu dalilai dake takaita himmar sojin kasar wajen murkushe kungiyar Boko Haram.

A ranar lahadi 9 ga watan Fabarirun 2020, mayakan Boko Haram da ake kyautata zaton cewar masu biyayya ga Abubakar Shekau ne, suka kai kazamin hari kan fasinjojin da suka kwana a garin Auno, mai nisan kilomita 25 daga garin Maiduguri, inda suka halaka akalla mutane 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.