Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta zargi Amnesty da yin karya a rahotonta

Ma’aikatar tsaron Najeriya ta yi Allah-wadai da rahoton da Amnesty International ta wallafa a ranar Juma’a, wanda cikinsa ta nemi hukunta wasu dakarun sojin kasar da ta tuhuma da kone wasu kauyuka a Borno gami da korar wasu mutane daga gidajensu, yayin maida raddi kan wani farmakin mayakan Boko Haram.

Sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya. Reuters
Talla

Yayin raddi kan rahoton, mukaddashin daraktan ma’aikatar tsaron Najeriya Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya zargi Amnesty ta yada rahoton karya a ci gaba da yunkurinta na bata sunan sojin kasar, abinda ya ce yin hakan tamkar goyon bayan ta’addanci ne.

Cikin rahoton, Amnesty ta ce ta tattara bayananta ne, bayan zantawa da mutane 12 daga cikin wadanda sojin Najeriyar suka konewa kauyuka 3 dake tsakanin Jakana da Mainok, a ranar 3 ga watan Janairun da ya gabata na 2020.

Kungiyar ta kuma ce, ta kara samun bayanai kan rahoton da ta wallafa ta hanyar hotunan da tauraron dan adam ya dauka, wadanda suka nuna yadda aka kone kusan komai a kauyukan 3 da suka hada da Ngariri, Matiri, Bukarti.

Sai dai ma’aikatar tsaron Najeriya ta bayyana zargin na Amnsety International a matsayin abinda ke nuna jahilcin kungiyar kan lamurran dake wakana a rewa maso gabashin Najeriya, da kuma adawa maras tushe da take nunawa dakarun Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.