Isa ga babban shafi
Najeriya-Tsaro

An yi wa shugaban Najeriya ihu a Maiduguri

Wasu mazauna garin Maidugri a jihar Bornon Najeriya sun yi wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ihu, sakamakon rashin kwanciyar hankali da ya ta’azzara a jihar a baya bayan nan.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Wannan ne karon farko da al’ummar Maiduguri suka fito karara suna nuna bacin ransu ga shugaban Najeriya.

Dubban al’ummar Maiduguri ne suka yi fitar dango a kan hanyar da ta nufi fadar mai martaba Shehun Borno, bayan sun samu labarin ziyarar shugaban kasar.

Wasu daga cikin matasan da suka fito sun tsaya a dukkan bangarorin tagwayen hanyoyin, yayin da wasu suka hau gadar masu tsallaka titi, kusa da kofar shiga birnin Maiduguri, wasu kuma suka girke kansu a kusa da makarantar kimiyya da fasaha ta Ramat Polytechnic, inda nan ne suka fara bayyana rashin jin dadinsu, lokacin da ayarin motocin shugaba Buhari ke shiga kwaryar birnin.

Shugaba Buhari, tare da wasu gwamnoni da manyan jami’en gwamnati sun sauka Maiduguri, babban birnin jihar Borno ne daga Addis Ababa, na Habasha, don yin ziyarar jaje ga gwamnatin jihar, sakamakon harin da kungiyar Boko Haram ta kai, wanda yayi sanadin mutuwar mutane 30.

‘Yan ta’adda da ke biyayya ga Abubakar Shekau sun kai wani kazamin hari a ranar Lahadin da ta gabata kan fasinjojin da suka kwana a hanya, daidai garin Auno, mai nisan kilomita 25 daga garin Maiduguri, sakamakon rufe hanyar zuwa Maidugri da sojoji suka yi.

Daga cikin wadanda abin ya rutsa da su har da wata mata mai shayar da jariri, wacce wuta ta kone ta da jaririn na ta kurmus, sakamakon banka ma wata tankar dakon man fetur wuta da maharan suka yi.

Maharan sun sace mutane da dama daga cikin fasinjojin.

Sai dai fadar gwamnatin Najeriya, ta bakin mai magana da yawun shugaban kasar Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ta ce, ‘wasu ‘yan tsiraru ne makiya kasar suka ba kudi don su yi wa shugaban kasar ihu’.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.