Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnati ta maka manoma dubu 70 a kotu

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta shigar da karar manoman jihar Kebbi har dubu 70 a kotu, bayanda suka gaza biyan Naira biliyan 17 da suka karba a matsayin aro daga gwamnatin.

Wani manomi a gonarsa dake yankin Dabua, a jihar Bauchi, dake Najeriya.
Wani manomi a gonarsa dake yankin Dabua, a jihar Bauchi, dake Najeriya. Afolabi Sotunde/Reuters
Talla

Cikin watan Nuwamban shekarar 2015 ne, shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani shiri mai taken ‘Anchor Borrower’ karkashin jagorancin Babban Bankin Kasar a jihar Kebbi, inda gwamnatin tarayyar ta tallafawa manoman da kudaden na aro.

Yayin zantawa da jaridar Daily Trust dake Najeriya, shugaban kungiyar manoman shinkafa ta RIFAN na jihar Kebbi, Muhammad Sahabi ya bayyana cewar, a halin da ake ciki manoma 200 ne kacal suka mayar da rancen da suka karba.

Shugaban manoman shinkafar ya kara da cewar kafin kaddamar shirin bada bashin noman na Anchor Borrower a 2015, manoman jihar Kebbi na noma adadin ton dubu 70 ne shinkafa a shekara, amma bayan kaddamar da shirin, adadin shinkafar da suke nomawa ya karu a 2016 zuwa ton miliyan 1 da dubu 200 a shekara guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.