Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa

Babbar Kotun Tarayya da ke birnin Abuja na Najeriya, ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same ta da laifin kashe mijinta Bilyaminu Bello.

Maryam Sanda tare da mijinta da ta kashe ta hanyar daba masa wuka
Maryam Sanda tare da mijinta da ta kashe ta hanyar daba masa wuka Daily Trsut
Talla

Mai Shari’a Yusuf Halliru ya bayyana cewa, akwai gamsassun hujjojin da suka bada damar ayyana Maryam a matsayin wadda ta aikata babban laifi.

Mai Shari’a Halliru ya yi watsi da ikirarin Maryam cewa, mijinta ya fadi ne kan buraguzan tukunyar Shisha a lokacin da suke fada a cikin gida.

Mai Shari’ar ya ce, hujjojin da aka tattara sun nuna cewa, ta daba wa marigayin wuka da zummar aika shi lahira.

Jim kadan ya yanke mata hukuncin kisan, Maryam ta yi kokarin tserewa daga dakin shari’a, yayin da danginta suka fashe da kuka tare da kururuwa, lamarin da ya haddasa hatsaniya a dakin shari’ar.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tuhumi Maryam Sanda kan aikata kisan kai da gangan a cikin watan Nuwamban shekarar 2017, yayin da rundunar ta bukaci yanke mata hukuncin kisa.

Mijinta ya kasance da ga tsohon shugaban Jam’iyyar PDP, Halliru Bello.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.