Isa ga babban shafi
Najeriya

Zabukan cike gurbi na gudana a wasu jihohin Najeriya

Zabukan cike gurbi na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi na gudana a wasu jihohin Najeriya.

Wasu jami'an hukumar zaben Najeriya INEC, yayin tantance masu kada kuri'a.
Wasu jami'an hukumar zaben Najeriya INEC, yayin tantance masu kada kuri'a. STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

Jihohin da zabukan cike guraben suka shafa sun hada da Imo, Akwa Ibom, Kano, Bauchi, Abia, Benue, Cross River, Kaduna, Niger, Sokoto da kuma Ogun.

A Kaduna, rahotanni sun ce an fuskanci karancin fitowar masu kada kuri’a a zaben cike gurbin kujerar dan majalisa jiha mai wakiltar sanga da Kagarko.

A Sokoto kuwa an samu fitar jama’a don kada kuri’unsu a zaubukan cike gurbin dake gudana a kananan hukumomin Sokoto ta Arewa da ta ta Kudu.

Zabukan sun hada da cike gurben kujerun majalisar jiha masu wakiltar Sokoto ta Arewa da Binji, sai kuma kujerun ‘yan majalisar tarayya a mazabun Sokoto ta Arewa da Kudu da kuma Isa da Sabon Birni.

Sai dai rahotanni daga kudancin Najeriya na cewa, zabukan cike guraben ‘yan majalisun ya gamu da cikas a wasu sassan jihar Cross River, inda wasu tsageru suka yi awon gaba da jami’an zabe, tare da kayan aikinsu a karamar hukumar Abi, inda ake zaben ciki gurbin dan majalisar wakilai.

Shugaban Hukumar Zabe INEC a jihar ta Cross River Johnson Alalibo ya shaida mana cewar kawo yanzu an sako jami’an zaben da kuma ‘yan sanda da masu bautarkasarda aka yi garkuwa da su, illa jami’I guda da ya rage.

A jihar Akwa Ibom kuwa, rahotani sun ce wasu sanye da kakin jami’an tsaro da ba a tabbatar da sahihancinsu ba ne, suka tsare jami’an Zabe a mazabar Ukana ta yamma, yayin zaben ciki gurbin dan majalisar wakilai, inda suka haramta musu amfani da wayoyin hannu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.