Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta yiwa Transparency raddi kan rohoton rashawa

Gwamnatin Najeriya ta maida martani kan rahoton kungiyar Transparency International da ya bayyana ta a matsayin kasar dake kan gaba wajen fama da matsalar cin hanci da rashawa a yammacin nahiyar Afrika, binciken da ta bayyana a matsayin maras tushe.

Rahoton Transparency International ya bayyana Najeriya a matsayin kasa ta 34 mafi fama da matsalar cin hanci a duniya.
Rahoton Transparency International ya bayyana Najeriya a matsayin kasa ta 34 mafi fama da matsalar cin hanci a duniya. Reuters Blogs
Talla

Ranar Alhamis 23 ga Janairun 2020, kungiyar Transparency International ta fitar da rahoton da ta saba fitarwa duk shekara kan matsayin kasashe da kokarinsu wajen yakar cin hanci ko rashawa.

Cikin rahoton ne kuma kungiyar ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta 34 a duniya wajen fama da wannan matsala, zalika kasa ta 146 cikin 180 a fagen kokarin magance matsalar ta cin hanci ko rashawa, bayan da ta samu maki 26 cikin 100 a 2019, sabanin maki 27 a shekarar 2018.

Wasu daga cikin dalilan da Transparency International ta zayyana a matsayin ginshikan bincikenta kan Najeriya sun hada da, rashin adalci wajen hukunta wadanda aka samu da laifukan cin hanci da rashawa ta hanyar kauda idanu kan wani bangare, musamman masu mulki da kuma attaijirai, a daidai lokacin da aka afkawa waninsa.

Batutuwa na gaba ta Transparency ta ce sun haddasawa yakar cin hanci da rashawa a Najeriya cikas kuma su ne rashin kyakkyawar alaka tsakanin wasu kafafen yada labarai da kungiyoyin farar hula, rashin kyakkyawar fahimta kan matsalar ta cin hanci da hanyyin magance ta, da kuma kazantar matsalar a muhimman sassan Najeriya da suka hada da tsaro, da kuma man fetur da iskar gas.

To sai dai Ministan Shari’ar kasar ta Najeriya Abubakar Malami da hukumar yakar rashawa ta kasar EFCC sun yi Allah-wadai tare da yin watsi da rahoton, wanda suka bayyana a matsayin maras tushe ko makama.

Auwal Musa Rafsanjani daya daga cikin masu fafutukar yakar matsalar cin hanci a Najeriya, yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, yace babbar hanyar samun mafita ita ce tabbatar da shugabanci nagari, da kuma bin salon babu sani ba sabo wajen gurfanar da masu lafi.

01:01

Najeriya ta yiwa Transparency raddi kan rohoton rashawa

Nura Ado Suleiman

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.