Isa ga babban shafi
Najeriya

Kun tuna lokacin da 'yan Najeriya miliyan 1 suka mutu?

Shekaru 50 kenan da kawo karshen mummunan yakin basasar da ya kashe sama da mutane miliyan 1 a Najeriya.

Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, jagoran fafutukar kafa Jamhuriyar Biafra fiye da shekaru 50 da suka gabata.
Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, jagoran fafutukar kafa Jamhuriyar Biafra fiye da shekaru 50 da suka gabata. Getty Images/Priya Ramrakha
Talla

Akasarin mutanen da suka rasa rayukansu a yakin na Biafra sun gamu da ajalinsu ne sakamakon fadace-fadace da barkewar cututtuka da yunwa a tsawon shekaru biyu da rabi da aka kwashe ana fama da rikicin.

A shekarar 1967 ne, Emeka Odumegwu Ojukwu, gwamnan sojin yankin gabashin Najeriya a wancan lokacin, ya zargi gwamnatin tarayya da nuna musu wariya da kuma kisan dubban ‘yan kabilar Igbo da ke rayuwa a arerwacin kasar.

A ranar 30 ga watan Mayun shekarar ce, Ojukwu ya ayyana gabashin kasar a matsayin Jamhuriya mai cin gashin kansa karkashin Biafra, wadda gwamnatin tarayya ta yi watsi da ita.

An samu barkewar yakin zubar da jini, inda gwamnatin tarayya ta aike da dakarunta zuwa gabashin kasar da zumar dakatar da yunkurin ballewar jama’ar Bifara daga Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta katse duk wani agaji da kuma hanyar shiga yankin na gabashin kasar har zuwa karshen yakin, wanda aka kawo karshensa bayan ‘yan Bifara sun mika kansu a cikin watan Janairun shekarar 1970.

A shekarar ta 1970 ne aka kawo karshen yunkurin fafutukar kafa Biafra, yayin da shugaban kasa na wancan lokacin, Yakubu Gowon ya ce, babu wanda ya yi nasara ko kuma aka ci galaban sa a yakin na basasar.

Bayan shekaru 50 da kawo karshen yakin, har yanzu da dama daga cikin al’ummar Najeriya na fama da radadin da yakin ya haddasa da suka hada da tsoffin mayakan da suka samu rauni, baya ga wadanda suka rasa ‘yan uwa da abokan arziki tare da asarar dinbin dukiyoyi da kadarori.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.